Shawara Ga Dalibin Ilimi


Ga ɗaliban ilimi ko mai son ilimi (na addini ko na boko, ko wata 'kwarewa' ('skill'))

1. Idan kana jin ka fi wani ilimi (saboda tarin iliminka, kwarewarka, shekarunka...), ba za ka taɓa ƙaruwa da iliminsa ba. Koda ya zo ma da sabon ilimi, girman kanka zai hana ka fahimta, balle har ka ƙaru. NEMAN ILIMI, BA NA MAI GIRMAN KAI BA NE (koda ilimin boko ne, ko wani 'skill').

2. Idan kana son koyo, ka zama mai sauraro (listener 👉bit.ly/3UCl93S), ba mai magana ba a lokacin da ake maganar ilimi (a makaranta, majalisi ko a cikin hira). Idan kana saurara, za kana jin abin da ba ka sani ba (sabo), idan kuma kana magana, kana furta abin da ka riga ka sani ne.

3. Idan aka ma karatun awa 1, a ƙalla ka sami awa 3 - 5 na bita da nazarin abin da ka koya (na karatun addini ne, ko na boko, ko gwajin wani skill), daidai da gwargwadon kaifin kwakwalwarka ko fahimtarka.

4. Gaggawa a neman ilimi (na addini ko na boko/duniya, ko 'skill'), na sa a samu ilimi maras inganci. Daga ƙasa ake yin sama, da kaɗan ake mai yawa. Ba girma ba ne, ɗauko manya-manyan littafai, ko wani babban 'skill' ba tare da ka yi na ƙasa da su ba.

Misali, mutum ya fara koyon littafan Fiqhu da ake nuna 'ta'arud' (cin karo) tsakanin fahimtar 'mujtahidai', ya bar asali littafan koyon ilimi (na ƙasa). Wannan na sa wa mutum girman kai, da neman kuskuren malamai. Misali, (kar ka duba shekarunka) idan ba ka taɓa zuwa neman ilimin 'Fiƙhun ibada' ba, a nan, a ƙalla, ka fara da 'Ahlari', idan ka kammala, ka shiga 'Ishamawi', sai 'Iziyya', sai 'Risala'... kuma ba gaggawa, a dai fahimci karatun, a iya aiki da shi.

A wajen koyon 'skill', a baya; Bahaushe sai ya zauna a wajen koyon sana'a na shekaru 15 - 20, tukun ake yaye shi (sannan ya kware). Kuma yana koya ne a mataki-mataki (duba littafin nan👉 bit.ly/WaneNeBahaushe1, shafi na 22)

5. Ana neman ilimin addini don a rayuwa bisa tsarin addini da tanadin lahira. Ana neman ilimin duniya don inganta rayuwa da amfanar da al'umma (a samu nutsuwar bautawa Allah don lahira). Dukkan biyun suna buƙatar kyakkyawar niyya.

Ibn Qayyim ya ce: "idan kana neman ilimi don abubuwa 3, to baka cancanci neman ilimin ba; (1) don ka ƙure ko kunyatar da jahili, ka nuna kai mai ilimi ne (2) don ka yi jayayya da malamai (3) don ka ɗora mutane kan fahimtarka, da karkatar da su kan abin da yake na asalin gaskiya."

6. A ƙarshe! Duk mai son koyon ilimi, ko kwarewa a wani abu na duniya, to ya koye shi daga wajen masani, kwararre a fanni (malami/mentor/expert), tare da biyayya, naci, tambayar abin da ba ka fahimta ba, da ƙanƙan da kai, koda ka fi shi yawan shekaru, ko kwalin karatu da tarin ilimi a wani fannin. Samun abokin karatu, shi ma na taimakawa sosai a wajen neman ilimin addini, ko na boko, ko wani 'skill'.

✍️ Aliyu M. Ahmad
28th Safar, 1444AH
25th September, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments