Gina Skill


Rubutunan yau kwanansa 74, har yanzu ba ka makara ba, rubutun nan zai maka amfani, musamman wanda yake 20s 👇🏻

Daga yau 8th May, 2024 ka sa a ranka za ka koyi wani skills, guda 1 kacal, tsawon wata 3:

Graphic design ne, ko
Video editing, ko
Coding da programming,
Content writing,
Social media management,
Cyrpto/Blockchain,
Data analysis, kai ko
Harshen Turanci (English)... da sauransu.

Za ka iya koyon 'BASICS' na ɗaya daga cikin dukkan waɗannan 'skills' online ko offline. Akwai wuraren da za ka biya kuɗi, wasu kuma kyauta ne ma a Youtube. Duk cikin waɗanda na lissafa za ka iya koya a cikin wayar hannunka, ba dole ne sai kana da computer ba. Mafi ƙarancin abin da za ka sadaukar a kullum 2hrs, da naci, da gwaji.

Kada ka damu ko ka yi gaggawar lalle-ilalla za ka samu kuɗi da skill(s) ɗin nan-da-nan kamar yadda wasu ke cewa ana samun kuɗi, kai dai yi ƙoƙarin ka koya ka kware. Idan ka kware, ka yi shuhura (ba kusa ba nesa), wallahi aiki sai kana gudunsa, kuma ka yi ta buɗawa da shuhura. Tun ana biyanka kaɗan, a hankali za a fara biyan da yawa.

Kuskuren da wani lokacin muke yi shi ne, buga-buga, ka kasa tsayar da zuciyarka a waje 1. Komai ka ji an ce ana samun kuɗi sai ka kama, da zarar ka ji wani sabo sai ka saki wancan ka kama sabo, ba ka nan, ba ka can, ka ɓata shekaru ba ka iya komai ba, ba ka kware a komai ba.

Ko kuma, da zarar ka fara koyo sai ka saka a ranka son yin kuɗi nan-da-nan, kana jin son zama irin mutumin da ya shekara 10 a wata harka, sai ka saka wa ranka damuwa.

• Ana samun kuɗi ne idan aka yi aiki,
• Ba a aiki sai kana da wani skill(s),
• Ba a samun 'skill(s)' sai an koya,
• Ba a koya nan-da-nan sai an ɗau lokaci.

Kana jin wata 3 ya maka tsayi a koyon 'basics' ko?

Shekara ma za ta zo ta wuce kana zaman banza, ba ka koyi komai ba, ba ka kuma sami aiki ko wata sana'a ba. Abokina, kana namiji dole ne sai ka yi aiki za ka sami kuɗi (sai 'yan ƙalilan masu nasibi).

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments