Ina buƙatar hutu!
Da gaske ina buƙatar ajiye wasu hidindumu da aiyuka da taƙaitawa kan wasu (muhimman aiyuka) domin lafiyata da kuma samar da 'timely services' ma ‘clients’ nawa tun kafin a zo ana cewa na haɗu da depression, ko na yi collapse a wani waje saboda stress-overload.
Musamman tun shiguwar 2024, nakan fita aiki (na internship) 8:00am, mu tashi zuwa 2:00pm. Daga nan ba gida zan je ko hutawa ba, zan wuce wajen aikinmu 'computer services centre' (Liberty), nan ba ma tashi sai 8:00pm (a ƙa’ida, amma wani lokacin mu kan kai har 9:00pm idan akwai aiyuka da yawa). Idan ina da 'facilitation' na 'program' (visual design, content creation, SMM...) kuma, nan ma 9:00pm zan hau ‘webinar’, har zuwa 10:30pm zuwa 11:00pm (wani lokacin, ba iya wanda nake ɗorawa a Facebook kawai nake ba, CSP ya fi yawa), da koyo da koyarwa.
Alhamdulillah! Ana samun rufin asiri, amma da matsala:
1. Screen time nawa yakan kai 10 – 18 hours a kullum, ko fiye, tare da ‘yan intervals na lokacin sallah, ko cin abinci ko wani uzuri. Illar dogon ‘screen time’ yana taɓa bacci saboda karantar sinadirn ‘melatonin’ sanadiyyar blue light na ‘screen’, da sanya damuwa da migraine mai naci. Counsellor ya ce har ‘carpal tunnel syndrome’ yana sa wa. Ba screen time ne ya fi damuna ba, distractions.
2. Ina kasancewa kusan kullum ‘online’ ne saboda ina tare da WiFi ne ba wai don ba wani abu da nake yi ba. Ina managing wasu shafuka a Facebook ma ‘clients’, gani na online kullum ba shi ke nufin ba na komai ba. Wannan na haifar da ‘perceived omnipresence’ ma wasu suna zaton kawai kana free ne ba abin da kake sai social media (saboda su suna hawan online ne a free time nasu ne), ba su san akwai aikin ‘social media management’ da yake buƙatar kulawarka ba a kodayaushe, sannan akwai software da kake aiki da su da ba sa aiki sai kana da ‘internet connection’.
3. Rubututtuka da yawa da nake ma, (wasu) tattaunawa ce da mutane ta DMs, sai na converting su zuwa ‘public disseminated contents’, shi ya sa suke da ɗanɗanon ƙarfafa gwuiwa, zaburarwa, gargaɗi….
4. Rabon da na uploading na social media portfolio na sana’ata ta ‘visual design’ a Facebook tun 2022, saboda distraction yana yawa, na takaita da ‘clients’ da ‘referral clients’. A kullum sai na workload list (to-do list) amma a lokuta da dama distractions kan hana ni cimmu su, sai ya zama ina kwana da bashin aiki.
A yanzu, ina da aƙalla contacts sama 7,557 a wayata, na ‘yan uwa, abokai, abokan karatu, clients, media mantees… A kullum zan ɗaga ƙira da bai gaza 100 ba, kada ka ce duk na aiki ne, a’a; wasu na neman wani hidima ne, assignments, editing rubutu, reviewing contents, neman alfarmar design, wani ya ce ga link na gaza cikewa ka cike min (yanzu-yanzu)... Matsalar ko idan ya turo maka da buƙata, bai san akwai wani ma ya turo ba, so, da wanne zan ji? Aikina, ko hidimdata wa mutane? Na rabo na da na zauna a waje, cikin unguwa, cikin mutane tun 2015, sai dai wucewa da sallama. Ina ta sa wa kaina son cimma koyon wani abu, ba lokaci (da matsala).
Misali, daga last week kwana 11 a jere (ban da ranar Lahadi) kullum sai na rubuta paper (jarabawa) na PGD, yawancin 2:00pm zuwa 4:00pm; da safe kuma (kafin lokacin exams) 9:00am – 11:00am ina prime lectures (na internship da nake), idan na dawo daga exams da yamma kuma 5:00pm – 6:00pm muna SJP fellowship, 9:00pm na fara facilitating program, a haka wani zai ƙira ka ba ka ɗaga ba, ko ya yi maka chat ba ka replying a kan lokaci ba, sai ya yi fushi (ko saboda kusanci, ko wani abu). Duk da ‘high stakes’ da ‘anxiety’ na jarabawa ba ya hana ni yin al’amuran rayuwata kamar kullum, amma idan abubuwa suka yi yawa dole jiki da kwakwalwa su amsa.
Kai! Ni ma fa mutum ne,
Ba machine ba!
Tun kafin damuwa ta taru ta yi min yawa, I have to adjust. Saboda stress da cognitive overload, ba zan manta da 25th November, 2022 ba a rayuwata, ranar da na haɗu da sakamakon stress overload na yanke jiki na faɗi a makaranta. A lokacin muna ‘final semester’ a jami’a, ga department (ina NASELS President), ga project research, ga aiki, ga mutune (tutorials na courses na 400L a aji, da lodge), ga relationship pressure… kada Allah ya maimaita min wannan yanayin na ‘stress-overload’ da ƙarancin shekaruna.
5. Matakin farko na gyara a rayuwa shi ne, KA MA FAHIMCI AKWAI MATSALA (ko kana kan wani kuskure), sai ka ɗauki matakin gyarawa kafin ta kwaɓe ma. Ah! Ni da kullum ina cikin faɗa wa wasu abin da ya dace, sai ni na gaza faɗawa kaina gaskiya? A’a! Jinya ba iya ta gaɓɓai ba ce, wata tana somawa daga tunani, damuwa, matsi... (cognitive disorders). Dole sai ka haɗa lafiyar gaɓɓai (physical), kwakwalwa da tunani (emotional/metal) da zamantakewa (social) tukun ka zama mai cikakkiyar lafiya (well-being). Saboda 'hyper-responsibility' da ƙoƙarin gyara zamantakewa (social), ba za a ignoring emotional well-being da zai iya haifar da physical issues ba.
Gaskiya dai ina bukatar hutu da focus. Idan ka fahimce ni, fa ni’im, idan ba ka fahimce ni ba, fa ni’im. Saboda ni na fi kowa kirki da son ganin mun ci gaba, it doesn’t make sense kuma na ignoring nawa kan. A yau idan na mutu ko na hadu da mummunan ciwo saboda ‘cognitive overload’, ba abin dai da zai tsaya a duniyar nan, wani ne ma zai replacing wajen biyan bukatar wasu. Yaushe zan sami lokacin hutu? Lokacin karatu? Lokacin kara koyo da fadada ilimin skills da nake da shi? Ni da ba ‘complacent’ ba.
Duk abin da ya shafi lafiyata, sirrina ne, I just explained it for clear picture of reason behind my detoxification. In sha Allahu daga 1st August, 2024 zan takaita hawa Facebook, zuwa 1st October, 2024 (lokacin na dawo gida da zama, full-time); sai dai ta Facebook Business Suite, shi ma don gudanar da aiyukana ne na ‘SMM’ da ‘visual designs’. Zan ma ajiye tablet da daya wayata na takaita da amfani da 1 kamar yadda counsellor ya b ani shawara a CBT. Lambata ce 07032219639, iya ta business ce don Allah.
A ƙarshe! Mu kula da lafiyar kwakwalwa, yana da muhimmanci sosai. In sha Allah zan sharing experiences na detoxification, ƙalubale da nasara in sha Allah a October, 2024.
✍🏻Aliyu M. Ahmad
12th Muharram, 1446AH
18th July, 2024CE
#AliyuCares #AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments