Abokin Huldar Kasuwanci

  

Wata alaƙar kasuwanci idan ta yi kyau, 'yan uwanta take komawa.

Idan alaƙa ta yi kyau, wani zai yi maka sanadiyyar arziƙin da wani ɗan uwanka na jini bai taɓa yi maka ba. Wani idan alaƙa ta yi kyau, sai ya jawo maka wasu don ka ƙulla alaƙar kasuwanci ko aiki da su, ka amfana da su, ka ci riba.

Idan kana sana'ar siya da siyawarwa, idan ba a zo an siye kayan naka ba, ta ya za ka ci riba ka iya juya uwar kuɗin, har ka rufawa kanka da waninka asiri?

Idan baiwa ko wani aiki ka kware, idan ba a kawo maka aiki ka yi aiki mia kyau an biya ka ba, aiki da baiwar taka za ka dafa da ci ne?

Koda wasa, kada ka wulaƙanta mai son ka da alheri, wanda zai zo wajenka siyayya ko kawo maka aiki. Mutum 1 zai iya jawo maka alherin mutane 10, mutum 1 zai iya sa ka rasa mutane 10. It doesn't matter ƙarami ko babban customer/client, wani mai cinikin ₦100, shi zai kawo maka mai yi maka cinikin ₦100k.

Iya mu'amala, gaskiya da cika alƙawari, samar da kyakkyawan kaya ko aiki za su taimaka maka wajen riƙe abokan hulɗa. Akasin haka, su watse, kai ne kuma da faɗuwa. Mu riƙe abokan hulɗa da kyau, mu riririta su, idan babu su, babu kasuwa, ita mai baiwarta ba za ka ci ribarta ba.

✍🏻Aliyu M. Ahmad
18th Muharram, 1446AH
23rd July, 2024CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments