Damuwa

• Mene ne yake damunka? 
Tun yaushe, tsawon wane lokaci?

• Ka taɓa zama ka yi tunanin dalilin shiga damuwarka? Idan ka san dalili, ka taɓa zama ka yi nazarin sakamakon aiyukanka (issues in you) da suka jawo maka shiga damuwa? Ko kuma tsautsayi ne da ƙaddara suka bi ta kanka?

• Ka taba nazarin darussan da wannan damuwar ta koya maka, ko dai kawai kana zaune me cikin damuwa? Sannan wane mataki ka taɓa ɗauka don maganin wannan damuwar?

Ɓacin rai da damuwa na ɗan lokaci ne. Abin da ya sa wasu ke ɗaukar lokaci cikin ɓacin rai ko damuwa, suna yi masa ban ruwa (watering) ne da yawan tunani. Ka riƙa tuna dalilin afkuwar abin a baya, maimakon ka bar shi ya wuce, ka mance da baya, ka rayu da yanzu.

Yawan tunani kan abin da ya sabbaba ma damuwa, misali cin amana, ko rashin wani masoyi (mutuwa), cin fuska, cusgunawa... (unresolved traumas) da sauransu, ba zai rage ma damuwa ba, sai dai kullum ka ci gaba da dauwama cikin damuwar, saboda kamar kana mata ban ruwa ne, ita kuma bishiya tana ƙara rayuwa da ban ruwa, har ta yi yaɗo.

Yawan damuwa har rage wa jiki kuzari (appatite) yake. Wannan ya sa, sau da yawa idan wani na cikin damuwa yake ramewa, a lokacin da (kuma) ya samu kwanciyar hankali da nutsuwa yake haske, kuzari da ƙiba.

Maimakon ka zauna kana ta tunani kan damuwa, ka shagaltar da kanka da maimaita 'ASTAGHFIRULLAH' (a kullum), a hankali zai maye gurbin yawan tunani, a hankali damuwarka za ta kau. Manzon Allah ﷺ ya koyar da mu addu'o'in dake 'coping' damuwa kala-kala, daga ciki akwai "اللهم اغفر لي ذنبي، واذهب غيظ قلبي، وأعذني من الشيطان", da wasu ma dama.

Maimakon ka zauna kana ta tunani kan damuwa, ka nemi agaji daga asibiti, mai damuwa majinyaci ne. Rashin lafiya hawa 3 ce, kuma kowacce akwai kwararru masu warware ta. Ta ɗaya, jinya ta jiki (physical) kamar zazzaɓi, ko wata cuta. Ta biyu, abin da ya shafi motsin rai (emotion) da tunani da kwakwalwa (mental). Sai kuma zamantakewa (social). Damuwa, matsananci fushi, ɓacin rai duk jinyoyi ne da suke buƙatar kulawar likita kamar yadda idan ka ji zazzaɓi, ciwon ido ko kunne kake zuwa asibiti domin neman magani. Akwai counsellor, neurophysiologist, psychotherapist, psychiatris... idan ka je OPD za su referring ka zuwa wajen wanda ya dace da kai.

Wata damuwar na buƙatar ka sami mai saurarenka, ka faɗa masa abin da yake damunka, sai ka ji sanyi a ranka saboda ka amayar da abin dake ranka, ko ka rubuce ta a takarda. Wata kuma har magani (meds) likita zai ba ka, wata bacci take buƙata, wata shiga cikin mutane, wata kuwa tadabburi... Likitocin kwakwalwa sun san me ya dace da kai. 

Ka bar damuwa,
Ka nemi maganin damuwa.
Damuwa na lalata maka rayuwa,
Abin da ya wuce, ya riga ya wuce.

✍🏻 Aliyu M. Ahmad
19th Muharram, 1446AH
24th July, 2024CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments