Cimma Buri


Wani ya ce:

• Manufa ba tare da wa’adi (cimma manufar) ba = Mafarki  

• Manufa + Wa’adi = (ita ce) Manufa ta gaske  

• (Ka sanya) Manufa + Wa’adi + Tsari = Niyya (ce kawai)

• Manufa + Wa’adi + Tsari + Ci gaba da aiki = Nasara  

• Manufa mai ma’ana + Wa’adi + Tsari + Ci gaba da aiki = Cikar muradi

Ma'ana dai, idan kana da wani buri, ya kamata ka sanya masa wa'adi, ka tsarin yadda za ka cimma wannan burin, ya zama na aiyukanka na yau da gobe suna nufatar cimma wannan buri. Ba kai kaɗai za ka sanya manufarka a gaba ba, wata tana buƙatar tallafin wasu, karatu, naci, jajircewa, ƙalubale, rashin sarewa...

Misali, domin cimma manufar karɓar shedar 'digiri' aka sanya tsari, mataki da wa'adi, tare da aikin koyo da gwaji tuƙuru a wa'adin da aka sanya. 

• Mece ce manufarka?
• Wane tsari ka yi domin cimma ta?
• Wane wa'adi ka sanya domin cimma manufarka? A ranar yau ne? Sati? Wata ko shekara?
• Aiyukanka na yau-da-gobe sun dace da cimma waccar manufar taka?

Ba ni za ka faɗa wa, kanka za ka ba wa amsa.

#AliyuMAhmad #AliMotives #RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments