Idan kana kallon 'skits' na Mark Angel da jimawa, za ka riƙa ganin Denilson Igwe tare da shi, abokinsa ne, amini; amma concept da idea na yin 'contents' na Mark Angel ne.
Daga baya da suka sami saɓani Denilson ya janye, saboda yana ganin duk abin da aka samu sai dai su raba 50/50 as a collobrator/partner ba supporter ba, har yake faɗi idan ya janye daga Mark Angel Comedy sai komai na Mark ya lalace, dama shi ne ke tallafa masa.
Yanzu maganar da ake, Mark Angel yana daga cikin top-10 content creators a Africa, No.1 a Nijeria. Yana da views sama da 2.5 billion a YouTube. A Facebook kaɗai Mark yana 22 million followers, Denilson da ya ware ya buɗe nasa channel 650k+ followers kawai yake da. Sai yanzu da Denilson ya ga nisan da Mark Angel ya yi masa tazarar ba kaɗan ba ce, sai ya fito gidajen jaridu yana hira wai shi ya taimaki Mark, amma Mark ya watsar da shi.
Rayuwar nan akwai darussa ga masu hankali da lura. Idan wani bai kyautata maka ba, ya kyautatawa wasu, saboda kai kaɗai ba zai gaza ya yi nasara ba. Ko Umar Bush aya ne, rayuwa ba shirin 'film' ba ce da wani zai tsara a rubuce yadda yake so ta kasance daidai da son ransa.
Rayuwar nan, kai za ka yi zaton kana taimakon wani, ba ka sani ba haskenka Allah ya ƙaddara yana tare da shi, da ka bar environment nasa sai ka disashe, koda abokinka ne, ƙaninka, ko ma yaronka. Kamar labarin wani mai kamfani da ya kori yaronsa saboda wani saɓani, sai duk customers da clients suka bi yaron da ya tafi, saboda don shi suke zuwa kamfani.
Yanzu tsawon shekara 8 Denilson yana rayuwa ne don ya ga Mark Angel ya gaza, ya lalace, amma sai ci gaba yake, shi kuma bai samu karɓuwa ba. A content 1, sai Mark ya sami reactions sama da followers na Denilson. Kada ka rayu da gilli, ba wanda za ka cutar face kanka, ka samawa kanka lafiya da mafita.
✍🏻Aliyu M. Ahmad
24th Muharram, 1446AH
29th July, 2024CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments