Neman Kariya



Kana ta fafutukar yadda za ka rufa wa kanka asiri, a wannan yanayin na matsi. Amma a haka wani yana can yana mana ƙulle-ƙulle, binne-binne, wani kuma na ɓata ma suna a wajen mutane, shi dai kwanciyar hankalinsa kawai, sai ya ga bayanka; ko ka bar masa duniyar, ko kuma ka tagaiyara tukun zai ji daɗi, hankalinsa ya kwanta.

Allah ﷻ da Manzonsa ﷺ sun fi ka sanin waye mutum, wannan ya sa Shari'a ta tanadar da wuridai na neman kariya daga sheɗanun mutane da aljannu. Don ba ka nufatar kowa da sharri, ba ya nufin wani ba zai ƙulla ma sharri ba (don akuya ba ta ci kura ba, kura ba za ta ƙi cin akuya ba). Ba ka ci haƙƙin kowa ba, ɗan abin da kake da shi ma bai taka kara ya karya ba, amma haka ganin rufin asirinka ke hana wani samun sukuni saboda ya ƙi yarda da kason Allah (wani ma ya fi ka samu). 

Dolenka ne ka nema wa kanka kariya ta hanyar yin wurudai na addu'o'i ingantattu daga Annabi Rahama ﷺ. A riƙa kiyaye wurudan safiya da maraice, dukkan motsinka, bacci, hawa abin hawa, shige da fice a gida, kasuwa, maƙabarta, bayi... sanyawa da cire sutura, cin abinci, tashi da zama, zaman majalissa... akwai wani zikiri da ake yi na neman kariyar Allah ciki, duba Hisnul Muslim misali, ALLAH ZAI KIYAYE MATUƘAR KANA KIYAYEWA (ولا يفلح الساحر حيث أتى) SAI DAI WATA JARABAWAR RAYUWA KUMA (وما هم بضارين به من أحد إلا بإذن الله). 

A duk lokacin da za ka yi bacci, yi ALOLA, ka karanta Ayatul Kursy, Ƙulhuwa, Falaƙi da Nasi, ka shafe jiki. Ka karanta Suratul Sajdah da Mulk (Tabara) ko a saurara a waya, a kwanta a ɓarin dama.

Allah ya tashe mu lafiya.

✍🏻Aliyu M. Ahmad
27th Shawwal, 1445AH
6th May, 2024CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments