Constructive dismissal/breakup
Wannan shi ne a Hausa ake cewa "kora da hali". Rimirimi kuna cikin shan soyayya, ba faɗa, ba wata matsala, ba ka san dalili ba, haka kawai sai masoyi ya sauya maka a lokaci guda, ya daina kula ka ('silent treatment' ko 'stonewalling').
Haka kawai zai daina maka chatting, ƙiran waya, tuntuɓa ta kowacce siga, kamar dai ya yanke alaƙa da kai faɗa maka ne kawai ba zai yi ba, kamar dai akwai 'emotional detachment'. Da kai za ka ƙira shi a waya ma, ba zai 'responding' ba, ko kuma ba zai biyo 'missed calls' ko replying 'chats' naka ba, sai dai ma ya fara kawo 'excuses' marasa kan gado, busy, busy... ko wani uzuri.
'Stonewalling' kyakkyawan 'red flag 🚩' ne da ke nuna akwai matsala, ya kamata ka yi ta kanka, ka san mutuncin kanka. Idan mutum ba ya ƙaunarka duk yadda ya kai ga ɓoye sai aiyukansa sun bayyana shi, sun nuna soyayyar ƙarya yake yi maka (discrepancy), aka ce LABARIN ZUCIYA, A TAMBAYI FUSKA, da zarar babu kai a cikin zuciya, aiyukan gaɓɓai za su sheda.
Bai kamata kullum sai kana takura kanka a kan soyayya ba, ya kamata soyayya ta zame maka salama ba tashin hankali da rashin samun nutsuwa ba. Duk wanda ya janye jikinsa daga gare ka ba tare da ka masa laifin komai ba, kai ma ka yi wa kanka mutunci da daraja, ka ba shi 'space'. A ka darjanta mutum, shi ne za ka tambaye shi, wane na maka wani abu ne na laifi? Yana cewa a'a, ka masa fatan alheri, kunyarka yake ji, ba zai iya ce wa a kawo ƙarshen alaƙa ba ne, kada ka wahalar da kanka kan shawo kan mutum ba tare da ka masa laifin komai ba.
Kai da kake matashi, maimakon ka fi damuwa da ya za ka gina kanka, haka kawai sai ka fi damuwa da wata aba soyayya? Uwar me za ta tsinana maka? Da ajinki da darajarki ki tsaya wani yana ta wasa da zuciyarki ƙanwata, shi ne ɗan autan maza ne? Ba wani mutum da ba za ka iya rayuwa don baya cikin rayuwarka ba, kafin ka san shi a baya ya kake rayuwa? Ba kai ne kake addu'ar zaɓin alheri ba, ba ka ganin rabuwarku alheri ce don samun shigowar alherin da kake roƙa? وعسى أن تكرهوا شيئا وهو خير لكم.
✍🏻Aliyu M. Ahmad
1st Dhul-Qidah, 1445AH
9th May, 2024CE
#AliMotives #AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #ConstructiveBreakup
0 Comments