Duk yadda ka kai ka nutsewa a kogin soyayya, kada ka kuskura HANKALINKA ma ya nutse. A kan ce "SO HANA GANIN LAIFI", amma kauda kai ma 'red flags' zai ja maka da-na-sani na har abada.
Ana iya samun wasu munanan ɗabi'u a mu'amalar soyayya a tsakanin dukkan masoya, a cikin maza ko mata, waɗannan munanan halaye ba su da nasaba da jinsi, ko ilimi, ko addini, ko shekaru, ko muhalli, ana iya samunsu a wajen kowa, sai wanda ya kiyaye son rai.
Misali, don ka ce kana son yarinya sai tana ta yi maka wasu ɗabi'u marasa kyau da rainin hankali amma sai ka dage ka kimtsa a zuciyarka wai ai jan-aji ne kawai irin na mata. Uhm! Who tells you? Ignoring the RED FLAGS 🚩 because you want to see the good in people will cost you later. Red flags 🚩 alamomin da ke bayyana a ɗabi'a na gargaɗi dake nuna wa abokin mu'amala, KA SHIGA TAITAYINKA!
Akwai misalan 'red flags' da yawa, suna bambanta daga mutum zuwa mutum, daga jinsi zuwa jinsi, misali:
• Da gaske ka nuna kana son yarinya, kana son ka tura gidansu amma sam taƙi amince wa, wai ba yanzu ba, RED FLAG 🚩 ne. Magana ba aure ba ce, za a iya magana a yi aure ko nan da shekara 10 ne. Taƙi ka ga iyayenta, kuma tana ci gaba da kula ka da ma wasu samarin, me kenan? Screening ake ma hala!
Ko kuma, ki dage saurayinki sai ya fito, ya turo iyayensa a san da zamansa a kogon zuciyarki, amma bawan Allah ya yi mirsisi, RED FLAG 🚩 ba za ki hankalta ba? Ki san matsayinki, ko ya turo, ko a yanke alaƙa kawai.
• Idan fa ba kai ka ƙira yarinya a waya ba, ko da za a yi sati ne ba za ta ƙira ka ba, kuma ba ta damu ba (emotional unavailability), RED FLAG 🚩 ne. Wannan yana nuna soyayyar ɓari ɗaya (one sided love) kake, kai ka damu, amma ba a damu da kai ba. Haka ke ma saurayin da kike masifar so, zai iya wata bai ƙira ki ba, wai yana 'busy', who tells you? Nobody is too busy. It's just a matter of priorities. If he want to find time for you, he will.
• Yarinya ta raina ka, ba ta jin maganarka ko umarninka, ko tsoron ɓacin ranka kwata-kwata. Da za ka ce kada ki yi abu kaza na ba daidai ba, sai ta yi, koda abun zai ɓata maka rai, REG FLAG 🚩. Babu soyayya idan babu martabawa, mace tana kiyaye umarnin wanda take so ko da a bayan idonsa don tsoron ɓata masa rai. Ta san kai ne za ka aure ta, amma tana kule-kule, ka ce ba ka so, amma ba ta ƙiya ba. Ko ka yi faɗan ma a banza. KA SHIGA TAITAYINKA! Don't ignore this RED FLAG 🚩.
• Yawan ƙarya, kisisina (manipulation), ɓoye-ɓoye (withhold information), rashin cika alƙawari (unrealibility)... duk alamu ne na ana rufarka, RED FLAG 🚩 ne. Yarinya za ta shirya da wani ya zo gidansu ya nemi aurenta, amma ba za ta sanar da kai ba. Idan ta sami mijin aure, kai kuma mene ne matsayinka? Ko ki yi magana da namiji zai turo gidanku, kun sa lokaci har kin faɗa a gida sai da lokacin ya zo ya fara kame-kame da ba da uzurai na ƙarya, sai an ce miki ba ke ba ce? Ba kula ba kuma ko akwai matsala ko alamar yaudara cikin alaƙarki da shi?
• Yarinya za ta yi laifi ko ta ɓata maka, amma da ka yi magana sai ta maida laifin kanka (blame shifting), ta dage sai ka ji cewa laifinka ne (guilt-tripping), RED FLAG 🚩 ne, koda tana son ka da gaske akwai matsala. Ɗaya daga cikin abin da yake ɗorar da alaƙa shi ne fahimtar juna. Rashin karɓar kuskure babban kuskure da tangarɗa a mu'amala.
• Ɗora maka nauye-nauye (financial exploitation), yarinya ta dage da ɗora maka buƙatu, ko karɓar bashin da biya za ta yi ba (exploitative borrowing). Ko ƙiranka ta yi a waya, har ka saba ka san wata buƙata ce, amma ba za ta iya ƙiranka ta gaishe ka ba sai tana da wata buƙata dai kai, ta mayar ka 'financial donkey.
• Ɓoye ka ma 'yan gidansu ko ƙawayenta (isolation tactics), kwata-kwata ba ta son alaƙarka da ƙawayenta ba ta son 'yan gidansu ko familynta su san da kai. Kai za ta furta maka cewa, "wai an ce kai zan aura, na ce musu ni ba kai ne mijina ba", RED FLAG 🚩. Kada ka ɗauka wannan wasa. Ko saurayi yana ɓoye ki ma familynsa ko abokansa, saboda me? Saboda ba ke ba ce!
• Breadcrumbing, saurayi ko budurwa su ajiye ku a matsayin 'backup', suna da wanda suke so da gaske, amfaninka kuma shi ne idan aka rasa na farko, a jawo ka. A wannan yanayi ba kai ba ne,ka san ba kai ba ne. Ba su so ka ba, kuma sun ƙi bari ka tafi wani ya so ka. Wata ta yarda tana saurayi, ta faɗa maka shi take so, amma kuma sai ta yi kishi da wata da za ka so.
• Kora da hali (constructive dismissal), wasu masoyan idan suka so rabuwa da kai, ba za su fito gar-da-gar su furta maka da baki ba, sai dai wasu ɗabi'unsu su saka fa fara tunani a kansu (gaslighting), misali, ƙoƙarin nisantarka (emotional distancing/detachement), ɓoye-ɓoye, raini... Misali, wata matar tana cire ka a ranka da jima tun kafin ta fara bayyana a zahiri. Ka kula! Tunaninmu ke samar da aiyukanmu, LABARIN ZUCIYA A TAMBAYI FUSKA, duk abin da mutum ya ɓoye a zuciyarsa yana bayyana ne a aiyukansa ne.
Da zarar ka ga alamun RED FLAGS 🚩 ka fara ƙoƙarin tserartar da kanka, ka kuma tsare mutuncinka. Kada soyayya ta sa ka wulaƙanta kanka, ko ka ce za ka nuna wata bajinta don a so ka. Ke ma ƙanwata! Mace da ajinki kada ki wulaƙanta kanka saboda saurayi, idan kika yi haƙuri Allah zai kawo miki mai son ki da gaske.
Mene ne GREEN FLAG 🇸🇦 kuma?
✍🏻 Aliyu M. Ahmad
14th Shawwal, 1445AH
23rd April, 2024CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments