Don ka sami saɓani da wani ko kana gaba da shi, ko ya ɓata maka, wannan ba zai tare masa wani rabo da Allah ya tsaga masa ba na ci gaban rayuwa, haka nan ba zai zama sanadin lalacewarsa ko shiga wani iftila'i ba. Me ka ɗauki kanka?
Akwai mutanen da ko wani iftila'i ne ya faɗawa wanda ba sa so, sai su raya a zuciyarsu saboda saɓanin dake tsakanin ko ƙiyayyarsu gare shi ne ya sa Ubangiji ﷻ ya jefa mutumin cikin wannan mummunan hali. Amma kuma da a kansu ne wata jarrabawa ta same su, ko wanda suke so; sai su ce ƙaddara ce (cognitive-bias).
Misali, saurayin da wata budurwa ta yaudara, kullum zai riƙa 'projecting' sai wani mummunan abu ya faru kan wannan budurwar, sai ta wulaƙanta, ta ƙasƙanta. Kwatsam! A ranar aurenta an zo ɗaukar amarya a mota sai suka yi 'accident' ta karye. Ko kuma bayan aure mijinta yake gana mata azaba, ko ta fito ta zama bazawara.
Ko kuma, wani malami da yake sukan ra'ayinka ya yi accident, ya yi kwatsa-kwatsa a hanyarsa ta komawa gida, ko kuma ya haɗu da wata mummunar jinya, sai ka yi zaton taɓa ra'ayinka ya sa ya faɗa wannan iftila'in.
A kullum ka zama mai tsarkakekkiyar zuciya, ka riƙa nufatar mutane da alheri, har wanda ya ɓata maka, shi ne halin mummuni. Yana daga cikin siffofi 4 da Ubangiji ﷻ ya yabi sahabbai kan 'dukiyar fai'u' cikin Hashr aya ta 10 da suke cewa: "ربنا اغفر لنا ولإخواننا الذين سبقونا بالإيمان ولا تجعل في قلوبنا غل للذين آمنوا", "Ya Ubangiji! Kada ka sanya gilli a zukatanmu kan ('yan uwanmu) waɗanda suka yi imani..."
Ya tabbata a wani hadisin Abdullah bin Amr ibnul 'As, wata rana Manzon Allah ﷺ suna zaune da sahabbai, sai ﷺ ya ce, "yanzu nan Ɗan aljanna zai shigo", sai ga Sa'ad bin Abi Waƙƙas ya shigo, aka yi haka har sukan sau uku.
Sai Abdullah ibn Amr ibnul 'As ya yi mamaki, wane irin aiki Sa'ad yake haka da har zai sami wannan matsayi? Sai ya nemi ya yi baƙunta a gidan Sa'ad don ya ga aiyukansa. Da dare ya yi, ya zuba ido ya ga ko Sa'ad zai kwana yana sallah (tahajjud), ya fa ga Sa'ad baccinsa yake sharɓa. Da safe ma bai ga Sa'ad na wata ibada ta musamman ba... Sai Abdullah ya faɗa wa Sa'ad labarin abin da ya kawo shi, ya kuma tambaye shi, ko yana yin wani aiki na musamman?
Sa'ad ya ce, "gaskiya ba ya yin komai face iya abin da ya gani (na sauƙe farali), ba ya riƙo (holding grudges), kuma ba ya yi wa kowa hassada kan ni'imar da Allah ya ba shi" (Musannaf na Abdurrazzaq 11/287).
Kai ma! Ka kwanta zuciyarka ba ta nufar kowa da sharri, ka yafe wa dul wanda ya ɓata maka, ka yi wa mutane fatan alheri, sai Ubangiji ﷻ ya sanya nutsuwa a zuciyarka, ya haska albarka cikin rayuwarka, ya ɗaukaka darajarka duniya da lahira. Riƙe gilli (holding grudges) cutar kwakwalwa ne (emotional distress), ka sama wa kanka lafiya.
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments