Ƙanwata!

Ƙanwata! NI MA MIJI in gaya miki babu addu'ar da na fi yi a kwanakin nan irin Allah ya azurta ni da mace tagari, wacce za ta zame min sanyin idaniya (ni ma namiji kenan). Ina ga ke?

Ƙanwata! Kada ki yi wasa da addu'a Allah ya ba ki miji magari. Ki yi da gaske! Ki rabu da masu cewa kina zuwa sallar 'tarawih' da 'tahajjud' don neman miji, eh! Ai a wajen Allah kike nema, ba a wajen kowa ba.

Ƙanwata! Akwai wata nasiha da mahaifiyyata ta taɓa yi min kan neman matar aure, ta ce, "ka ƙaddara Allah ya yi za ka shekara 70 a duniya, idan ka yi aure kana da shekara 30, zaɓar macen da za ku rayuwa tamkar zaɓar yadda za ka ƙare shekarunka 40 ne a duniya. Idan ka auri 'yar bala'i ka shiga bala'i, ka haɗu da hawan jini da 'depression'. Idan ka samu salaha asirinka ya rufu". To! Ina ga ke mace za ki dogara ki zauna a ƙarƙashin wani?

Ƙanwata! Idan ma kina da wani buri a 'future' bai wuce aure ba. Burin karatu ko aiki a wajenki ke mace duk suna bayan aure. To laifi ne don kin roƙi Allah 'future'rki', Allah ya baki miji nagari?

Ƙanwata! Muma maza muna roƙon 'future', mu roƙi nasibi, aiki mai kyau, rufin asiri, ke kuma mece ce taki 'future'? Ki roƙi tsarin Allah daga namijin da zai sa kina 'HIDE MY ID'.

Ƙanwata! Duk lokacin da za ki yi addu'a, ki roƙi Allah ya ba ki miji nagari, aure shi ne burin 'ya mace. A gidan aure za ki huta ko ki shiga bala'i, ki roƙi alheri.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments