Bayan Ramadhan


Alamar ba a karɓi ibadarka ita ce, ka koma aikata aiyukan alfasha a bayan sallah (wasu ma a ranar sallah).

Reflect! 

Sahabban Manzon Allah ﷺ da aka yi wa alƙawarin aljanna ma tun a duniya, ƙara ƙai mi ma suka yi na aiyukan ibada (Tirmidhi, 3747). Manzon Allah ﷺ tsayuwa yake da daddare har dudadugansa na kumbura, Nana A'isha رضي الله عنها na ce masa ﷺ ya shi da aka gafartawa gaba da baya amma yake wahala haka? ﷺ sai ya ce, "افلا اكون عبدا شكورا" (Bukhari, 4837).

A cikin hadisin ƙudsi, Ubangiji ﷻ da kansa ya kwakwanta bayin da ya yarda da su, yake son su: "فإذا أحببتُه كنتُ سمْعَه الذي يسمعُ به , وبصرَه الذي يُبصرُ به , ويدَه التي يبطشُ بها ورجلَه التي يمشي بها , وإن سألني لأُعطينَّه , وإن استعاذَني لأعيذنَّه..."

Ma'ana, bawa idan ya sami yarda da soyayyar Ubangiji ﷻ dukkan gaɓɓansa za su riƙa yi wa Ubangiji ﷻ biyayya ne, su aikata abin da Allah ke, da barin abin da ba ya so.

Kenan, idan ka samu kusanci da yardar da Allah aiyukan gaɓɓanka ne za su nuna. Idan kuwa ka koma saɓawa Ubangiji ﷻ wannan alama ce ta taɓewa, da alama kuma ba ka sami abin da ake nema ba a Ramadhan, saboda 'ƙasdin' Ramadhan ya yi maka tarbiyya, kuma ba ka ɗauki tarbiyyar ba. Duk iskanci da ka haƙura aikata shi a kwana 30, manufar a koya maka za ka iya rayuwa ƙalau ko babu shi.

Allah ya masa mana ibada.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments