Neman Zaɓi Allah


Kana namiji, me ya kai ka ƙiran sunan 'yar mutane a addu'a? Ka roƙi Ubangiji ﷻ ya yi maka zaɓin alheri. Ko wannan yarinyar da ka nace, kake tsananin so, idan ba alheri ba ce, Allah ya raba ku da salama, ya maye ma da wacce ta fita alheri.

Sau da yawa sai ka so mutum, alhalin shi ba alheri ba ne a gare ka, ko kuma kai ba alheri ba ne a gare shi. Mutum nawa ne suka haɗu da 'depression', wasu 'hawan jini', wasu suka shiga rigima da 'yan uwansu kan wanda suke so? Ba alheri!

Na wa aka yi waɗanda masoyan nasu suka zame nusu sanadiyyar shiga wani iftil'in rayuwa, ko ma suka rasa rayukansu? "وعسى أن تحبوا شيئا وهو شر لكم" in ji Ubangiji ﷻ. Mutum nawa za ka so, a lokacin da kuke soyayya kowa zai rufe mummunan halinsa da aibunsa, sai bayan an yi aure halin kowa ya bayyana?

Ke ma haka ƙanwata!

Ubangijin da za ku roƙa alheri, shi ya san abin da ke ɓoye cikin zukata, shi kuma ya san me gobe za ta haifar (ghaibu). Ko aiki, muhalli, abin hawa ka roƙi Ubangiji ﷻ mafi alheri. MAI NEMAN ZAƁIN ALLAH BA YA DA-NA-SANI. Allah ya yi mana zaɓin alheri, kada ya bar mu da wayonmu 🤲 

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments