Yadda ake lissafin 1/3 na dare ana lissafin ne daga faÉ—uwar rana (Maghrib) rana zuwa fitowar 'Alfijir'.
Sannan, lissafi da agogo yana bambanta daga yanki zuwa wani yankin. Misali, a garinmu rana tana 'ghurubi' a 6:30pm, 'alfijir' kuma na 'ƙetowa' a 5:10am, kenan darenmu yana da 10hrs 40mins ko 640mins (a dunƙule).
Sai mu raba wannan 10hrs 40mins zuwa gida 3 (1/3), daga 6:30pm zuwa 5:10am. Kowanne kaso zai É—auki 'sulusi' (1/3):
• Daren farko: 6:30pm - 10:03pm
• Dare na biyu: 10:03pm - 1:37am
• Dare na uku: 1:37am - 5:10am
Kowannen yankin dare ya ɗauki 213 minutes. Daga 1:37am zuwa 5:10am shi ne kason 'sulusin dare' na ƙarshe. Wannan shi ne lokacin da aka fi so a yi 'tahajjud'. Ko ba ka samu damar jona 'tahajjud' a jam'i da sauran mutane ba a masallaci ba, kana da damar yin naka nafilolin a tsakanin wannan lokacin (sai ka yi lissafi da garinku).
Allah Shi ne Mafi sani.
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments