Bacci 🛌🏻

Idan kana da niyyar halarta 'sallar tahajjud' a daren yau, ya kamata a ce ƙarfe 9:00pm - 10:00pm ka yi bacci, a ƙalla ka samu yin bacci na 3hrs - 4hrs kafin tashi sallah tsakar dare (1:00am+). Dole ne yanayin baccinka zai canja, saboda yau za ka sami 'first night effect'. Wannan na nufin, zai shafi hatta gudanawarka ta gobe (routines).

Amma ba ka kwanta ba sai 12:00am, ko ma ba ka yi baccin ba kwata-kwata kana latsa waya. An kammala tahajjud around 4:00am ka ɗan kwanta ba ka tashi ba sai after 6:00am, ba ka sami sallar Asuba, ka yi asarar 'farilla' don ka riski nafila (asara kenan).

Ko kuma, ba ka yi 'planning' na baccinka ba, saboda jikinka bai saba ba, ka dawo bayan sallar Asuba ka yi dogon bacci, kuma ka karya alƙawarin aiyukan mutane da za ka yi da safiya, ka tashi kusan 11am - 12pm, ga rana, sai ka kasa aikin kirki a ranar, hatta yanayi ka sai ya canja, ranka yana ɓaci babu dalili.

A shekarunka 18 zuwa sama, yana da kyau ka riƙa baccin da bai gaza 7hrs - 9hrs ba a kullum. Idan ka yi bacci 4hrs kafin tashi tahajjud, kayi 2hrs - 3hrs da safe, ka ɗan yi ƙailula (nap) bayan azahar, jikinka zai sami kuzari. Idan ka yi tsara baccinka, ba za ka takura ba, za ka sami sallar tahajjud cikin nutsuwa da kuzari (ba ana sallah kana gyangyaɗi ba), jikinka zai huta, jikinka zai zama cikin kuzari da rana, dole zai ka ɗabbaƙa sabon yanayin bacci (bedtime routine) saboda 'sleep familirization'. 

Ubangiji ﷻ na cewa cikin Rum aya ta 23 "ومن آياته منامكم بالليل والنهار وابتغاؤكم من فضله ۚ إن في ذلك لآيات لقوم يسمعون". Ma'ana: "Kuma akwai daga cikin ayoyinSa, barcinku a cikin dare da rana, da nemanku ga falalarsa. Lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu saurarawa".

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments