General Market


#GeneralMarket

Ya ce: 

"Baby! Auren nan da na ce ƙarshen December, gaskiya a yi haƙuri sai al'amura sun fara daidaita tukun".

Ta ce: "Hubby! Me ya sa?". Ya ce: "BQ na gina 50ft x 50ft, 3-bedroom bungalow a December, 2023, ₦7.5m ne, yanzu ya doshi ₦15m, hakan ma idan ana cikin aiki wani abu bai ƙara kuɗi ba".

Baby ta sunkuyar da kai, ta ce: "Hubby! To yanzu ya za a yi kenan?...". Ya ce: "Ni a wacce shekara ma aka haife ki?" Baby ta ce: "2003".

Ya ce: "To Wallahi! Kuɗin sadaki kaɗai a yau, a kai kuɗin sadaki da lefe, har da canji a lokacin da aka haife ki. A 2003, $1 = ₦128, mafi ƙarancin sadaki bai fi ₦8,355 ne (1.0625kg na dinar a Malikiyya).

A yau sadaki kaɗai, $65.36 ne, ₦131,784 kenan. Idan kika lissafa $1 a 2003 a kan ₦128 a cikin ₦131,784, za ki sami  $1,029.5 a 2003, kin ga darajar ₦131,784 a 2003, daidai yake da ₦1,956,168.75 (₦1.9million) a yau".

Ya ce: "Baby kin gane lissafi kuwa?".

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives #AliyusFiction

Post a Comment

0 Comments