Fushi


Fushi

Yana daga cikin ladabi a duk lokacin da ranka ya ɓaci, ka shiga cikin FUSHI, to ka kame bakinka ka yi shiru. Manzon Allah ﷺ ya yi wa sahabbai wannan tarbiyyar, "إذا غضب أحدكم فليسكت" (Musnad Ahmad, 2135).

Fushi kan tono abun da ka bunne a zuciyarka na tsawon shekaru, ka furta cikin fushi, kuma daga baya kuma ka dawo kana da-na-sani.

Idan rigima ta haɗa da kowaye, gwamma a ce kai matsoraci ne, ba iya cewa komai ba, da a ce ka faɗi abin da zai saka ka da-na-sani daga baya. Ko tunzura ka aka yi, kada ka mayar da martani cikin fushi. Fushi kan sa ka fara tone-tone, ƙage, ƙazafi... domin a lokacin fushi notin hankali ne ke kwancewa.

Manzon Allah ﷺ ya kwatanta mutumin da yake da jarumta, shi ne mai iya mallakar kansa a lokacin fushi, MALLAKAR KAI A LOKACIN FUSHI SHI NE JARUMTA (Bukhari, 6114). Daga cikin abubuwan da suke sauƙar da fushi, akwai kame baki (yin shiru), idan kana tsaye ka zauna, ka kuma riƙa maimaita a'uziyyah ko wani tasbihi, tahmidi... kowa dai wani zikiri cikin ranka.

Imam Ali bin Abi Talib رضي الله عنه kan ce, "أول الغضب جنون وآخره ندم" Ma'ana, "fushi yana farawa ne da hauka, ya ƙare da nadama ne". (Adab Al Shari'iyya 1/183). Alaƙa nawa ce ta lalace sanadiyya mayar da martani cikin fushi?

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments