Cyber-trolling
Ta fuskar psychology (nazariyyar halayyar ɗan Adam), yawan yin cyber-trolling alama ce ta rashin lafiya (ta kwakwalwa).
Cyber-trolling shi ne yawan neman rigima, tsokana, da zungurar mutane da faɗa don ka ɓata musu rai, ko don ka jawo su riƙa magana a kanka. Yawaita cyber-trolling alama ce ta shiga yanayin damuwa (SPD), kuma babbar alamar dake bayyana haka ita ce, neman rigima, kamar yadda na ambata a sama. Mai wannan matsalar yana da buƙatar ganin 'psychiatrist' ko 'psychotherapist' don karɓar CBT ko wani 'therapy' na musamman.
Koda an tuhumi da mai trolling a kotu kan cyberbulling, za a fi karkatar da shi zuwa asibitin jinyar kwakwalwa (psychatry) maimakon ɗaukar hukunci, saboda 'case' ne da majiyanci (sadist).
Saboda cyber-trolling na da alamomin boardlines, wanda yake cikin 'SPD' ba ya jin daɗin, sai shi ma ya ɓatawa wasu rai. Akwai misalan irin wannan da yawa, daga cikin ɗaliban ilimi ko yaran 'yan siyasa a 'social media'.
Idan ɗalibin ilimi ne, zai riƙa zaƙulo wasu mas'alolin addini da suka saɓa da ra'ayin wasu, ko zaƙulo kusakuran wani malami ya yaɗa, kawai don jan rigima da waɗanda suke ganin ƙimar wannan mutumin. Ba a biyewa irin wannan saboda kamar mai taɓin hankali ne ya jefa ka da dutse, maimakon ka wuce, sai ka biye shi kuna jefe-jefe (ka zama kamar shi kenan).
Cyber-trolling yana taɓa fuskar (image) mutum sosai, za a yi ma shedar maras son zaman lafiya, ko maras kunya da sauransu. Ga wand ya fahimci 'psychology' zai ma kallon maras lafiya. Sai dai ga wanda yake cikin yanayin 'sadistic personality disorder' (SPD), yana ga normal ne, kamar mai jinyar taɓin hankali ne ya yi tsiraici, ko yana surutai ma marasa ma'ana, yana ga normal ne a wajensa.
Cyber-trolling yana da ɗan bambanci da cyber-bullying, saboda bullying zagi ne, ko cin mutunci kai tsaye, shi kuma wancan neman tsokana ne da neman rigima akai-akai.
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives #FasaharZamani
0 Comments