Ko ka sani?


Idan ka kai ɗanka koyon karatu wajen malami mai zafi, ɗanka zai zama mai zafi. Idan malaminsa mai girmama mutane ne, zai tashi a mai mutunta mutane... kalar malami, kalar ɗaliban da zai raina. 

👉 Kuma ka duba 'samples' na malamai ko a 'social media', ka yi muƙaranar ɗabi'un malaman social media da 'traits' na malamansu. Irin kalar malaman da mutum yake cin mutuncinsu a social media, irin su ne dai malaminsa ke zungura.

Idan ka kai ɗanka koyon sana'a, ubangidansa yana da cika alƙawari, da sannu yaronka zai koyi halin cika alƙawari. Idan mai wasa da hankalin mutane ne, shi ma zai koyi 'manipulation tactics'. Idan ubangidansa yana da kazar-kazar, yaronka zai tashi ba kasala, ba wasa, haka akasin haka.

BA KARATU KAƊAI KO 'SKILLS' AKE KOYA BA, HAR DA TARBIYYA A ƊABI'A. 

Idan ka auri mace salaha, za ta yi 'passing' salihancinta ga 'ya'yanta (musamman mata), haka ma 'yar bala'i. Saboda yawan zama tare yana gadar da halaye. Ka lura da a wajen wa mace ta tashi? Mahaifiyyarta? Ko kakarta? Ko wata mace ta daban? Akwai tsammani 60% na kwaikwaiyon ɗabi'a tsakanin 'ya da uwa, ko wacce ta tashi a wajenta (ya danganta da yanayin zamansu). Kalar matarka, kalar 'ya'yanka (Kendra, 2023).

Ka san lokacin da ka fara magana da harshen Hausa? A'a, tashi kawai ka yi ka gan ka kana yi. Mene ne dalili? Saboda muhalli (linguistic environment) da aka haife ka, Hausa ake yi. Kuma ka bi ta wasu matakai sukan 6 - 7 (tsakanin haihuwarka zuwa shekara 2, 3, 4...) kafin harshen Hausa ta zaune ma a harshenka.

Addini fa? Shi ma tasowa cikinsa ka yi ka ga ana yi a gidanku. Idan gidanku Izala ake, 99% approbability a ɗan Izala za ka tashi, haka sufanci da sauransu, ko wasu addinai na daban.

Bi'a (environment) yana da matuƙar tasiri ma tunani (thoughts), tunaninmu kuma ya samar mana da ɗabi'u (habits), ɗabi'unmu su samar da mu, a mutanen kirki, ko na banza. Duk tarbiyyar da mutum ya samu daga tushe kuma (asas/basic), tana da wahalar sauyawa idan ya girma. Ba yi aure, yi aure ba ne kawai, wacce irin al'umma za ka samar a gobe?

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments