Wata Ɗabi'armu...


Wata ɗabi'armu da ya kamata mu gyara!

Ban son yi magana a kan irin wannan, amma na mangantu da yawa... Mutane da yawa kamar ba sa son mutane su zama MUTANEN KIRKI, jira suke ka yi KATOƁARA ko ka LALACE su yi ta TSINE ma, ka zama 'topic of discussion'.

Kasancewarka Mutumin Kirki (a yadda ake zato), shiriyar Allah ce ba zaɓinka ko wayonka ba ne. 

Shi wanda yake kan ɓata (a saninka) ko aikata assha, abin TAUTASAYI ne, KAMAR MUTUM NE MAI JINYA da yake buƙatar MAGANI: fata da addu'ar shiriya, nasiha da shawarwari cikin hikima (العلاج النفسي). Ban da TSINE masa, GULMA ko yaɗa ɓarnarsa, ban da kuma ƙoƙarin sanya masa sunaye marasa daɗi da baƙaƙen maganganu.

Bukhari (3308) da Muslim (2643) sun ruwaici hadisin Abdullahi bin Mas'ud رضي الله عنه, Manzon Allah ﷺ Yake cewa:

"فوالذي لا إله غيره، إن أحدكم ليعمل بعمل أهل الجنة حتى ما يكون بينه وبينها إلا ذراع فيسبق عليه الكتاب، فيعمل بعمل أهل النار، فيدخلها، وإن أحدكم ليعمل بعمل أهل النار، حتى ما يكون بينه وبينها إلا ذراع، فيسبق عليه الكتاب، فيعمل بعمل أهل الجنة، فيدخلها."

"Na rantse da Sarkin da ba wani sai shi! Inda ɗayanku zai kasance yana aikata aiki irin na ƴan Aljanna, har sai ya kasance tsakaninsa da tsakaninta bai tsawon zira'i ɗaya ba, sai littafi ya yi rinjaye a kansa, sai ya yi aiki irin na ƴan wuta, sai kuma ya shiga wutar.

Inda ɗayanku zai kasance yana aikata aiki irin na ƴan wuta, har sai ya kasance tsakaninsa da tsakaninta bai tsawon zira'i ɗaya ba, sai littafi ya yi rinjaye a kansa, sai ya yi aiki irin na ƴan Aljanna, sai kuma ya shiga Aljannar."

• Abu na farko da za mu lura da shi, ta iyu wanda yake a taɓe yana aikata wani aiki da Allah zai iya duba ya masa rahama, kamar kyautatawa iyaye, ko tausayi, ko yana tashi tsakar dare yana neman gafarar Ubangiji kai kuma baka sani ba. 

A cikin Bukhari (3321), Manzon Allah ﷺ Ya ba da labarin wata mace (KARUWA) da ta shayar da kare, sanadiyyar wannan Allah Ya gafarta mata.

• Abu na biyu, yawan yada labarin ɓarnar wani, yana rage masa zunubi, kai kuma yana ƙara maka nauyi zunubi. Idan aka je Alƙiyama sanadiyyar gulmarsa da kake yaɗawa a nan duniya, za a ɗauki 'laifinsa' a baka, a ɗauki 'aikin alherinka' a ba shi (exchanging) [Sahih Muslim, hadisi na 2581].

• Abu na uku, zai yi wuya ka fiye surutu laifukan mutane, ba tare da Allah Ya jarrabe ka da misalin abin da kake jinginawa bayinsa ba, ko a karan kanka, ko a cikin 'ya'yanka/zuri'arka.

Shiriya ta Allah ce! In ba za ka iya yiwa taɓaɓɓe nasiha ba (cikin hikima), ko addu'ar shiriya, ƙauracewa gulmarsa ko wa'azi mai dulmiyya ya fi ma alkhairi. FATA NAGARI LAMARI NE. 

Allah Ya tabbatar da mu kan hanya madaicciyya, amin.

✍️ Aliyu M. Ahmad
23rd Shawwal, 1443AH
24th May, 2022CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments