Ajiya Maganin Wata Rana


A yau, idan aka sace ma wayar hannunka, ko ta faɗi, shin kana kuɗin siyan irinta ko madadinta? 

Kana jan adaidaita, ko sana'a da computer ko wata na'ura, idan suka lalace a yanzu-yanzu, ko suka daina aiki a yanzu, kana da 'alternative', ko iya siyan madadinsu a yanzu-yanzu, ko sana'arka tsayawa za ta yi cak? 

Wane tanadi kake yi wa irin yanayin da zai iya zuwa kwatsam a rayuwa?

Wannan yana daga cikin 'Precautionary Motive' na John Maynard Keynes (1883-1946) kan adana wani kuɗi don tunkarar matsalar da kan iya tasowa bagatatan. Kana aiki da 'computer', 'adaidaita sahu' ko wani 'machine' kana samun kuɗi da su, amma ba ka taɓa lissafin cire masu wani hasafi cikin abin da kake samu ba daga jikinsu ba. Sai rana 1 idan suka ƙone, ko suka lalace, ko ta sami matsala aiyukanka su tsaya cak, kuma ba ka da wani tanadi a ƙasa.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments