Fiction da Non-Fiction


Daga 2017 zuwa yau shekara nawa ne?

A 2016/2017 Akwai yarinyar da wani abokina ya so, so na gaske, so na son aure, amma ka san me zai ba ka mamaki?

Wai ta karanta wani 'novel' (na manta sunan littafi), akwai wani character 'Hashim', ɗan talaka ne, ya faɗa soyayya da wata 'A'isha' tun a yarinta. A lokacin da ta fara girma, manyan mutane sun yi ta so su aure ta ta ƙi, har ce mata ake ita matar manya ce. 

Har raba su an sha yi, amma suka ƙi rabuwa. Daga ƙarshe ya tafi Abuja leburanci, har ya haɗu da wani Alhaji, ya sama masa aiki. Ita kuma da riƙon amana ba ta auri kowa ba, har sai ya dawo, ya aure ta, ya ɗauke ta suka tafi.

Katsam! Baiwar Allahr nan ta haɗu da wani saurayi mai suna 'Hashim' (a gaske), ta manne masa, za ta yi adopting irin abin da karanta a 'novel'. Ta yi ta wulaƙanta masu son aurenta da gaske. A 2018, shi wancan abokin nawa ya yi aure, ita kam har yanzu tana jiran 'Non-Fictional Hashim' ya yi kuɗi.

Mu rinƙa nazari! Rayuwar 'fiction' daban, rayuwa zahiri daban. Labarin 'fiction' marubuci ne zai juya ƙaddarar me zai faru a cikin labari. Labarin gaske (reality) aiyukanmu ne za su samar da sakamako.

Don wata ta wulaƙanta ka akan batun soyayya, ba ya nufin za ta shiga wata matsala, kai kuma za ka yi nasara a rayuwa, ka yi kuɗi. Saɓaninka da wani ba zai tauye masa wani rabo da Allah ya sa nasa ba ne. Haƙƙinka daban, rabon arziƙin Allah daban.

Ba sai ka cutar da kanka da ƙiyayya ba, ko ƙullacin kowa ba, mutum ya ɓata ma, ko ya yi ma ba daidai ba, kowa abin da ya shuka zai girbe, a duniya ko lahira, duk daren daɗewa. Har wanda ya cuce ka, ba lalle ya wulaƙanta ba. Haƙƙinka daban, rabon da Allah ya tsaga masa daban.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments