Auren Zamani


A hankali ita kanta manufar auren gushewa take. Gida shi ne tushe al'umma da tarbiyya, da zarar ya tarwatse, tarbiyyar al'umma ta ɗaiɗaita.

Idan har mace saboda ta sami aiki daidai ko fiye da na namijinta raini zai shiga tsakani, mene ne manufar aure tunda tana iya ɗaukar ɗawainiyya kanta? Shi kaɗai ne manufar aure?

A hankali mun koma girmama kuɗi, kuɗi shi ne mutunci. Da a za aure ka don kana da makudan kaɗaɗe sai ka karye, sai a daina ganin girmanka, to dama kuɗinka aka aura. Kuɗi kawai muke girmamawa?

Ana ƙarfafawa mata gwuiwar su yi karatu mai zurfi, musamman a ɓangaren lafiya don taimakawa 'yan uwansu mata. Ana ƙarfafa mata guiwa su yi sana'a don dogaro da kai saboda zamani. Su tara kuɗin da za su iya ɗaukar ɗawainiyya kansu da yaransu ko babu maigida.

Amma labarai daga tajibar mutane da yawa da suke auren hamshaƙan mata tana ba ni tsoro. Wayonka ba ya zaɓa ma mata, ko ke miji; sai dai ka yi addu'a dacewa. Jahilai futuk za ta iya fatattakar farin cikinka, mai izza da wadata ta zame ma sanyi ido, and vice versa.

Astagfirullah! Ba mu da labarin aure da zaman auren Manzon Allah ﷺ da Nana Khadija عليها السلام? Kubra attajira, mai shekaru da tarin dukiya.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments