Aboki


Ban ga mai asara ba kamar mutumin da yake yana da aboki, abokin nan Allah ya yi masa baiwar ilimin addini, har wasu suna taso daga wasu wurare na nesa suna zuwa É—aukar karatu wajensa, amma kai girman kai da raini sun hana ka sunkuyar da kai ka koya, ka koyi karatun addini a wajensa, kawai saboda shi É—in abokinka ne? 

Ban ga mai asara ba kamar wanda yana aboki, abokin nan yana da wata sana'a. Cikin mutanen da suke kula masa da sana'arsan nan har da waɗanda suka girme shi, ga ka (kuma kai) kana zaune 'jobless' ba za ka iya zuwa ka ce masa kana son za ka yi aiki a ƙarƙarshinsa ba don ka rufawa kanka asiri, kawai don abokinka ne? Akwai waɗanda abokan ne ma za su nemi su zo su yi aiki tare, sai su 'rejecting' kawai saboda ba za su iya zama a ƙasan abokan da Allah ya ɗaukaka kafin su ba.

Ban ga mai asara ba kamar wanda yana da aboki, abokin nan yana da wata baiwa da kwarewa (skills) da ake iya neman kuÉ—i da ita, misalin digital skills, tailoring, carpentery..., wasu mutanen (ma) daga nesa suna zuwa wajensa su koya, su koma su je su kafa kansu, amma kai saboda girman kai ai abokinka ne ba za ka koya ba a wajensa, kuma kana zaune 'jobless', saboda da kawai shi abokinka ne.

Don abokinka ne, wanda kuka taso tare, ba za ka (iya) koyar abin arziƙi a wajensa ba? Amma ba za ka ji kunyar tambayar shi kuɗi ko bashin kuɗi, ko aron sutura ko abin hawa ba, don Allah ina tunani a nan?

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments