Tarbiyya a Jiya da Yau


A matakin farko, iyaye su ya kamata su zama masu jin koken 'ya'yansu, su kuma jiɓanci lamuransu na rayuwa.

Tsakanin iyaye da 'ya'ya akwai haƙƙoƙi, ba iya na ciyarwa, ko biyan kuɗin makaranta, ko ba su wajen kwanciyya ba ne kaɗai, a'a... 'ya'ya suna da sauran haƙƙoƙi a kan iyaye.

Cikin Adabul Mufrad, Abdullahi Ibn Umar رضي الله عنه yake cewa: "إنما سماهم الله أبراراً لأنهم بروا الآباء والأبناء كما أن لوالدك عليك حقا كذلك لولدك عليك حقا." 

Idan ya kasance tsakaninka da 'ya'yanka ba jituwa, ba ka iya zama ka saurari damuwarsu; a'a, tsakaninka da 'ya'yanka kawai, daga FAƊA, HANTARA sai bayar da UMARNI, sai SANYA SU FARGABA da TSORO, babu WASA da DARIYA, babu JA A JIKA... to tabbas 'ya'yanka za su nesance ka, har lokacin da kake tsananin buƙatarsu (lokacin tsufa). Za su kuma maida abokansu sune abokan shawararsu a duk abin da ya taso musu na rayuwa. Idan ba a yi dace ba, wasu abokan, za su kai 'ya'yanka ga halaka.

Akwai bambanci tsakanin bada TARBIYYA da kuma TAKURAWA. Wasu iyayen 'takure' 'ya'ya suke, su hana su sakat, da sunan kulawa; wannan ba 'tarbiyya' suke yi musu su ba. A bada tarbiyya, ana duba yanayin zamani (yau) da kuma muhalli (wurin zama) domin samun daidaito wajen bayar da tarbiyya.

A wata nasiha, Imam Ali ibn Abi Talib (RA) cikin إغاثة اللهفان (M2/265) yake cewa: 

لا تربوا أولادكم كما رباكم أباؤكم فقد خلقوا لزمان غير زمانكم

"Kada ku yi renon 'ya'yanku kamar yadda iyayenku suka rene ku, domin an halicce su ne a wani zamani ba irin naku ba" 

Na biyu, yadda 'ya'yan zamani suke da wayewa ta abubuwa da dama, ya wuce yadda (wasu) iyayen ke tsammani. Shi ya sa wasu iyayen ke mamaki sosai, idan aka ce, wane yaronka/yarinka suna kaza-da-kaza marasa kyau.

Mu sani! Duk wayonka, tsawatarwa da ƙoƙarinka ba zaka iya shiryar da 'ya'yanka ba, sai Allah Ya so su da shiriya. Idan ka sanyawa 'ya'yanka tsoron Allah, ko ba ka nan ba za su aikata ba daidai ba. Idan ka sanyawa 'ya'yanka tsoronka, a gaban za su nutsu, amma a bayan idonka za su aikata abin da suka ga dama. Ana kuma neman taimakon Allah cikin haka.

Allah Ya shiryar mana da zuri'a.

5th Dhul-Qaadah, 1443AH
5th June, 2022CE.

#Iyaye #Tarbiyya
#RayuwaDaNazari
#AliyuMAhmad

Post a Comment

0 Comments