Silar Mugunta

1. Da mahaifiyyarta ta rasu, sai ta koma wajen kishiyar mahaifiyyarta. Ita kuma kishiyar, irin matan nan ne da iya 'ya'yansu suka sani.

Yarinyar ta sha wahala sosai, duk kusan aikace-aikacen gidan ita ce ke yi, girki, shara, wanki da wanke-wanke, har wahala ta zame mata jiki. Ta kuma ta tsare 'yarta ta cikinta daga waɗannan wahalhalun, ba abin da take; daga zuwa makaranta, sai dai ta ci, ta sha, wani lokacin kayan sawarta ma, waccar 'yar kishiyar ke wanke, a tunaninta, hakan gata ne take yi wa tata 'yar, tana muguta da kishi da 'yar kishiyarta.

Da aka aurar da su, ita waccar marainiyya ta iya girki, gyara gida, wanki da wanke-wanke da duk sauran ɗawainiyyar cikin gida. Ita kuma 'yar lele an tarbiyanceta ne daga ci sai sha, sai kwanciya, hakan ya ja mata matsalar a gidan aure, aurarrakinta ya yi ta mutuwa.

------

2. Shi ma Ɗankawu, bayan da mahaifinsa ya rasu, sai ya dawo hannun ƙanin mahaifinsa. Ƙanin mahaifi na gidan bulo, 'ya'yansa na zuwa makaranta, shi kuma aka saka shi aikin leburan ƙarfi da yaji. Shi ne aiki a gidan bulo, bugawa, ɗorawa, sauƙewa, har da ma wasu aikace-aikacen gidan...ya dai sha wahala matuƙa, da kyar ya iya kammala sakandire.

Bayan da ƙanin mahaifin ya rasu, sauran 'ya'yan ƙanin mahaifin ba abin da suka sani na yadda ake sarrafa kasuwancin wannan gidan bulo (ba su da experience). Da aka rabe gado, suka bi ta kan kasonsu suka albozarantar. Shi kuwa yaron ya kafa nasa gidan bulonsa da ɗan abin da mahaifinsa ya bar masa tun yana yaro, ya ci gaba da nema daga falalar Allah. Wani lokacin ma, wurinsa 'ya'yan kawu ke neman taimako.

A lokuta da yawa, cikin gidaje ko wurin aiki, wasu na ga suna yi wa wani mugunta da matsawa, alhalin ba su san tarbiyya da hora shi suke ba shi ba, na abin da zai amfane shi a gaba.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments