Fahimtar Ɗabi'u da Halaye


Ka karanta a nutse!

Idan da za ka fahimci yadda mutane ke kallon al'amuran rayuwa, da ɗabi'u da ra'ayin mutane kan wasu lamura za su daina ba ka mamaki.

Kada ɗabi'ar mutane ta ba ka mamaki a kan SOYAYYA da ƘIYAYYA. Idan muna son mutum, alherinsa kurum muke kallo, idonmu zai rufe akan kuskurensa da gazawarsa; soyayyarsa ce za ta yi rinjaye a zukatanmu.

Wannan ya sa a duk lokacin da wani malami alal misali ya yi tuntuɓe, za ka ga wani zaƙaƙuri (intellectual) na jikinsa na ba shi kariya, saboda ya san alkhairansa da yawa, to akan me ta dalilin kuskure ɗaya za a soki malaminsa, masoyinsa? Kun gane? Bayan ga alheransa da yawa da mu ba ma gani, ko ba mu san su ba.

Wannan ya sa a duk lokacin da muke son mutum, komai zai yi mana na kuskure, za mu ba shi uzuri, saboda tarin alheransa gare mu da muka sani. Waɗanda kuma suke sukarsa a lokacin, wataƙila iya wannan kuskuren suka sani, ba su san wani alherinsa da ya ɓuya gare su ba.

A lokacin da muke ƙin mutum kuma, dama idon ya rufe, kuskure da gazawarsa kawai muke nema. Ba mu zauna da shi ba (tsawon lokaci), balle ma mu san alheransa. Wannan kuwa a siyasa ne, ko a addini ko a zamantakewa. Misali, mace (budurwa) idan ba ta son mutum, duk alheransa da ɗawainiyyarsa a kanta, za ta rufe ido kan wani kuskure 1 don ta rabu da shi. Amma wanda take so, komai gazawarsa, za ta yi ta ba shi kariya da uzuri saboda soyayya.

Game da yadda muke kallon lamuran duniya kuwa, muhallin da muka taso, shekarunmu, jinsinmu, ƙarfin tattalin arziƙinmu, zurfi ilimi da tunaninmu, tajriba da gwagwarmayar rayuwa duk suna mana tasiri. Tunanin talaka daban yake da mai kuɗi, haka na ɗan birni da mutumin karkara, ko na wanda ya yi makaranta boko zalla, da wanda ya haɗa boko da addini, da kuma wanda ya yi karatun addini zalla, hatta waɗanda suke sana'o'i daban-daban... dole tunaninmu ya bambanta,

Misali, Hassan da Hussaini da aka haifa ta tatso ɗaya, a rana ɗaya, suka taso tare, suke komai na rayuwa tare. Hatta makaranta tun daga 'nursery' har jami'a tare suke. Da za su tafi NYSC sai aka tura Hassan Lagos, Hussaini aka tura shi a Sokoto; zaman shekara ɗaiɗai da za su yi a wurare mabambanta sai ya canja musu tunani daban-daban dangane da rayuwa, saboda sauyin muhalli, da sauyin mutanen da kowa ke mu'amala da su.

Mutumin da karatun fiƙhunsa a Ahlari ya tsaya, 'bacci' kala ɗaya 'طويل ثقيل' ya sani wanda yake warware alola; amma wanda ya ɗora da Ishmawi ya san '2' ne, طويل ثقيل da قصير ثقيل kuma an kasa bacci gida 4, zurfin karatu kenan. Haka wanda ya zurfafa a Iziyya, Risali, Muktasar, Bidaya, I'ilam, Mudawwana...da 'shuruh' nasu, zai san mas'alolin fiƙhu da zurfi fiye da wanda ya taƙaita, shi ma a iya Malikiyya ne.

Wanda ya karanci Islamic Studies zalla, komai na rayuwa ta fuskar addini zai na masa fassara. Haka wanda ya karanci tattali, siyasa, doka (law) ko kimiyyar lafiya... maslahar rayuwa ta fuska addini, tattalin arziƙi, muhalli, dokar ƙasa ko lafiya, ta fuskar da kowa ya samu tarbiyyar ilimi, da ita zai fassara rayuwa.

Wanda yake 'sunni' ya karanta Tarikh na Imam Attabary, Nihaya na Ibn Kathir... zai riƙi abin da ya karanta ne a matsayin hujja. Amma ɗan shi'a ya karanta Waƙ'at Siffin na Ibn Muzahim ko Kitabul Irshad na Mufid, abin da ya ga cikin waɗancan littafan sune hujjarsa kan waƙi'a'o'in bayan wafatin Manzon Allah ﷺ, tasirin abin da muke karantawa kenan.

Kaso mafi yawan abin da muka riƙa na addini, a matsayin aƙida ko manhaji, ko mazhaba, gidajen da muka taso suna da tasiri matuƙa. Da wuya ka ga Battijane, wanda mahaifansa ba tijjanawa ba ne, ko kuma akwai tijjanawa a unguwarsu da yawa. Za ka iya samun 'Salafi' a Nijeriya, wanda abokai ko sauyin wurin zama ya masa tasiri.

Ba ka taɓa tunani me ya sa ka tashi da harshen Hausa a bakinka ba? Ko me ya sa ka iya Hausa bayan wani harshe da kake magana da shi a muhallin da kake? Me yasa wasu kalmomi ke bada ma'ana mummuna a muhallinka, amma wani karin harshen ke da ma'ana mai kyau?

Idan mutumin Sokoto ya ce ma Kano a gabas take, don kana zaune a Jigawa, kafin ka ƙaryata shi ka fara duba, a ina mai wannan maganar yake? Sokoto na yamma da Kano, kai kuma kana zaune gabas da Kano. Abin da yake daidai a wajen wani, ba lalle ya kasance daidai a wajenka, saboda waɗancan dalilan na sama.

Wannan ya sa 'yan mazhabar 'relativism' (nisbawiyya) ke fassara cewa, ba wani abu haƙiƙa gaskiya, sai abin da ya bayyana gare ka, ta fuskar maslahar rayuwarka. 

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments