Ranar HIV/AIDS ta Duniya 2023


Wani rubutu ne (na gyara) da na taɓa rubutawa wani wanda a lokacin aurensa aka gwaji yana da HIV, abin ya dame shi sosai, ya ce na ba shi shawara, don ji yake kamar ya yi 'suicide' saboda da damuwa:

Me yasa idan an ce HIV gaban mutane ke faɗuwa? Akwai cututtuka da suka fi HIV illa da kisa sosai, ciwon hanta (HBV) da ake iya ɗauka ta haɗa jiki, ta gumi, ga sikila, luikemia, ciwon daji (cancers) balle HIV yau is no more 'kanjamau', za ka iya rayuwa da ita har mutuwa ba tare da ramewa ko kwanciyya don ciwo ba matuƙar mutum na shan magani (ART), kuma kyauta ne a manya asibitoci.

Akwai wani labari da na taɓa karanta na wani mutumin Liberia, ya yi jinya sosai har ta kai ga an masa gwaje-gwaje ciki har na da HIV. Bayan sakamako ya fito, aka ga 'positive', cikin sati biyu ya rame, ya kwanjame, ya kasa cin abinci.

Daga baya aka gano cewa, kuskure aka yi a bayyana result na test, ba na sa faɗa masa ba, na wani ne daban. Aka sake masa test aka nuna masa don ya tabbatar, ya ga 'negative', ya dawo ya ci gaba da rayuwarsa normal. 

Babban abin dake sa mu kyamatar HIV, yawanci ana ɗebo ta ne ta jima'i, saboda tana daga cikin STDs masu saurin yaɗuwa ta hanyar jima'i. Duk da akwai sauran hanyoyi na tsautsayi da mutum zai iya ɗiban HIV. Wasu kuma mazajensu ne, ko matayensu za su kwaso a wani waje, su goga musu, wasu ma fyaɗe za a musu, a goga musu jaraba. Kar mu kyamaci 'yan uwanmu da suke ɗauke da ciwon, ita kanta damuwar ta fi HIV ƙanjamar da mutum.

2.10% na cikin adadin mutanen Nijeriya 'yan tsakanin shekara 15 - 49 suna ɗauke da HIV, aƙalla sama da mutum 2.2 million kenan. Za ka iya halarta kowacce cibiyar kula da masu HIV/AIDs a maka gwaji kyauta don tabbatar da matsayin lafiyarka.

Mu daina kyamatar masu ɗauke da HIV, ba a ɗaukarta ta numfashi ko haɗa jiki, sai dai ta jima'i, ko amfani da allura guda. HIV ba mutuwa ba ce, za ka iya ci gaba da rayuwa kamar kowa matuƙar za ka kiyaye ƙa'idojin shan magani. 

Za ka ƙara fahimtar manufar Shari'ar Musulunci tunkuɗe ɓarna da cutarwa na haramta zinace-zinace, luwaɗi da maɗigo, waɗanda sune hanyoyin da aka fi yaɗawa da kwasar STDs, cikin har da HIV da ta fi kaurin suna. Abu ne mai kyau mu ilmantar da kanmu yadda za mu kare kanmu da cuttuka masu yaɗuwa, mu yi karatu, mu tambayi masana, muna kuma kiyayewa.

Mu kiyaye!
Allah ya kiyaye mu.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives 
#WorldAidsDay

Post a Comment

0 Comments