Wa Take So?


Kai take SO da gaske? Ko
Abin hannunka take so? Ko
Son yadda kake sonta take? Ko
Son alfarma take yi ma? Ko
Aure ne kurum take son yi...

Idan tana son ka da gaske, ba wani dalili na tarin dukiya, kyau, ilimi ko nasaba da zai zama shi ne dalilin son. Idan waɗannan ne sune (kawai) hujja (unconditional love), idan ta samu wanda ya fi ka kamalarsu, za ta zaɓe shi, ta bar ka.

Idan tana sonka da gaske, ba wani saɓani ko gazawa da zai girgiza sonka a zuciyarta. Ko kai ka mata laifi, lallaɓa ka za ta yi, ka huce, don ku shirya. Amma ta ma laifi, kuma ta yi fushi, ka ƙi sauƙar da kai, kai ma ka san sauran.

Idan abin hannunka take so, da zarar ka damke hannu, son ya ƙare, har sai ka yi 'subcription'. Dalilin da ya sa ba a ce ba a sonka ba, saboda ana morarka ne, da zarar ba mora, ba so, 'tit-for-tat'.

Idan yadda kake sonta take so, tana son buga misali da kai a wajen ƙawaye; cewa, kana mata soyayya iri kaza, ko irin copyn soyayyar da take kallon a finanai (burge ta kawai kake).

Idan so alfarma ne, shi ne irin son da take nunawa saboda alaƙa ta jini, ko makwaftaka. Za tana ba ka attention ne don kar a ce tana ja ma aji, ko tana da girman kai, ko ta ƙi ka, ga ka na gida.

Idan son aure ne, sai bayan aure za ta fahimci, auren take so, ba kai ba, wataƙila saboda ƙawayenta sun yi aure, ko ta sa a ranta cewa, a daidai lokaci kaza za ta bar gidansu; daganan sai ta fara ma shaƙiyanci.

Idan ba ka iya bambance waɗancan ba, ka roƙi Allah ya ba ka mai sonka da gaske, har yau ba a sami malamin da ya iya nazartar cikekken halin mata ba, balle ya gano haƙƙinin abin da suke so kam, babu! (Rieger, 2025). Komai falsafarka, wayewarka, iliminka, dabararka... ka nemi zaɓin Allah.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
#TitForTatLove #SonGaskiya #NemanZabinAllah

Post a Comment

0 Comments