Guji Taƙlidanci


Shawarar da zan ba ka matashi,

Ka yi karatu,
Ka yi karatun addini,
Ka yi karatun boko,
Ka yi karatu,
Ka ci gaba da karatu...

Ka yi karatu don neman gaskiya, kar ka bari taƙlidancin ƙungiyanci yana rufe ma ido. Musulunci aka ce ka yi, ba ƙungiyanci ba!

Ka yi karatu, ka fahimci, kowacce irin da'awa mutum ya zo da ita, zai (iya) samun masu goya masa baya, akwai (kuma) waɗanda zai yi wa tasiri.

Duk wannan rikicin ƙungiyanci da ake, a cikin kaso 24% na adadin mutanen duniya da suka yarda Musulunci ne addininsu. Kaso 76% na sauran mutanen duniyar ma, ba su ma yarda da Musulunci a matsayin addini ba.

Ka buɗe zuciyarka, kar ka yarda wani ya bautar da kai da ƙungiyanci, iya abin da yake na ƙungiyarsa ne daidai, duk wanda ya saɓa masa maƙiyi ne, duk abin da ya saɓa masa kuskure ne. Kuma kowa yana komawa ne ga nassi, ya yi tawili daidai gaskiyarsa ko son zuciyarsa.

وأنا منا المسلمون ومنا القاسطون فمن أسلم فأولئك تحروا رشداً

Idan ka nemi shiriya, ka nemi gaskiya da gaske, Allah zai shiryar da kai kamar yadda ya shiryar da Salamul Farisi. Idan ka haƙiƙance da taƙlidanci, gaskiya za ta zo ta wuce, kana manne da iya abin da ka riƙe.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments