KALMA 'GAY' A CIKIN 'THE QUEEN PRIMER'


1. Tsohuwar ma'anar 'gay', tana nufin 'farin ciki', 'nishaɗi'..., amma kafin ƙarni na 17th - 18th. 

2. Daga baya, farkon 19th, ake danganta ta ga 'yan luwaɗi' (LGBT), sai aka sami 'semantic drift', sai ta koma 'pejorative word', daga kyakkyawar ma'ana, zuwa mummuna*.

Idan ka buɗe dictionary a yau, na littafi ko a waya, sabuwar ma'ana ce ke zuwa a farko, kafin tsohuwar ma'ana, wanda hakan ke nufi an fi amfani da ma'ana ta farko (¹), kafin wacce ta biyo ta (²) a 'lexicography'. 

* Akwai misalan kalmomin da a baya munana ne, suka canja zuwa kyawawa (melioratives) kamar 'nice' (wawa), amma yanzu 'mai kyau'.

3. Saboda sabuwar ma'ana kalmar 'gay', 'social media' tana 'filtering contents' dake ɗauke da irin wancar kalmar ta 'gay'. Duk 'profile' ko 'device' da yake da 'parental control', ba ya iya accessing 'adult-restricted contents', cikin har da wanda yake da 'keyword' na 'gay' ko 'queer words'. 

4. Idan yara za su iya 'accessing internet' don duba ma'anar kalma, 'gay' a Google, 'illicit contents' ne za su fito saboda sauyin ma'anar kalmar tsawon lokaci, sai dai idan akwai 'parental control' a kan device ɗin.

Ba Dr. Bashir Aliyu ne ya fara magana kan 'The Queen Primer' ba kaɗai, an jima ana zancen kan littafi har a Ministry of Information da NBC, saboda sadduz zari'a (toshe ɓarna). Littafin ba shi da wannan hadafin na yaɗa LGBT, saboda lokacin da aka wallafa shi, ba a amfani da kalmar a matsayi 'luwaɗi', kuma a 'rythm' na 'poem' aka sa kalmar da ma'ana 'nishaɗi'.

5. Ban ga abin musu, jayayya ko jahiltar da mutane kan abin da za a naƙadinsa a ilmance, kuma kowa yana da fuskar da zai kalli abu, ta fuskar ma'ana (semanteme), amfani (context) ko tarihi tsatso (entym).

#AliyuMAhmad #AddiniDaRayuwa
#RayuwaDaNazari #AliyuTheLinguist
#TheQueenPrimer

Post a Comment

0 Comments