Tanadin Azumi


A yau Asabat 6th Rabi'ul Thani, 1445AH (21st October, 2023) watan azumin Ramadhan na bana (1445AH) sauran kwana 140 (sati 20 kenan, ko wata 4 da kwana 20).

Idan a gidanku akwai matasa 3 zuwa 5, za ku iya wani asusu da za ku farantawa iyayenku cikin sati 20 a Ramadhana na bana.

Misali, a sati 20, duk sati kowannenku yana ajiye ₦1,000 ko fiye, a sati kuna da ₦3,000 ko ₦5,000, a wata kuna da kusan ₦12,000 ko ₦20,000, kafin Ramadhan ya zo kun tara ₦60,000 (ku 3) ko ₦100,000 (idan ku 5 ne).

Da ₦60,000 ko ₦100,000 (ko fiye), za ku farantawa iyayenku sosai, a kuma rage na kayan abincin buɗa baki da sahur a Ramadhana.

Haka nan idan kai magidanci ne, za ka iya wani asusu na musamman don tanadin azumi, ta yadda za ka sauƙaƙawa kanka ta fuskoki da dama.

Idan ma shirin sadaka da tallafawa wasu mutane ne, za ka iya fara tanadi tun yanzu. Ɗan kaɗan da za kana ajiyewa, zai taru ya yi yawan da zai ma amfani mai yawa a gaba.

اللهم بلغنا شهر رمضان واجعله لنا شهر خير وبركة وتوبة وغفران.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives 

Photo credit: ₦airaland Forum

Post a Comment

0 Comments