Addini ba iya yawan bauta (ibada) da zakiri da nesantar saɓo ba ne kaɗai, wannan naka ne (karan kanka) tsakaninka da Ubangiji ﷻ.
A addini, akwai kyautata mu'amala tsakaninka da bayin Allah kuma (su ma suna da haƙƙi a kanka) mutanen da ka sani, da waɗanda ba ka sani ba.
A cikin Adabul Mufrad (117), Abu Hurairah رضي الله عنه ya ce, wani mutum ya tambayi Manzon Allah ﷺ game da wata mata mai yawan nafilfili (sallar dare, azumi da sadaka), amma tana cutar da makwaftanta da harshenta. Manzon Allah ﷺ ya ce, "لا خير فيها، هي من أهل النار", ma'ana "BA WANI ALHERI A TATTARE DA ITA, 'YAR WUTA CE".
Sai wannan mutumin ya sake tambayar Manzon Allah ﷺ game da wata mata, ita kuma tana iya sallolin farilla (kaɗai), tana sadaka (kaɗan), amma ba ta cutar da kowa. Manzon Allah ﷺ ya ce, "TANA DAGA CIKIN MUTANEN ALJANNA".
Wani hatsari kuma game ga cutar da mutane, idan an je lahira kana mutumin kirki, ba ka taɓa zina ba, ba ka taɓa sata ko kisan kai ba..., sai ka wayi kanka a filin Alƙiyama da zunuban alfasha da fasadi.
A cikin Sahih Muslim, hadisi na 2581; Manzon Allah ﷺ ya tambayi sahaibai رضوان الله عليم cewa, "shi kun san waye fallasasshe?" Sai suka ce, "shi ne mutumin da ba shi da zinare da azurfa." Sai Manzon Allah ﷺ ya ce: "Fallasasshe a ranar tashin Alƙiyama, shi ne wanda zai zo da sallah, da azumi da zakkah, sai dai kash! Ya zagi wancan, ya ci naman wancan, ya yiwa wancan kazafi, ya ci dukiyar wancan, ya zubar da jinin wancan, a nan za a riƙa ɗauko waɗancan kyawawan aiyukan ana bawa waɗancan da ya zalinta; idan kyawawan aiyukansa suka ƙare, sai a fara ɗebo laifukan waɗancan ana jibga masa, a ƙarshe ya wurga shi cikin wuta (wa'iyyazubillah).
Imam Al-Qurtubi (612 - 671AH) a cikin الجامع لأحكام القرآن [m. 18/199] ya ce: "idan ka kasance cikin waɗanda ke cin haƙƙin mutane da harshe, suke ghiba, buhtan ko annamimanci da sauran iri-iren laifuka da suka shafi haƙƙin wani, tubansu yana karɓuwa ne idan ka nemi yafiyar wanda ka yiwa laifi ya yafe ma."
✍️ Aliyu M. Ahmad
5th Rabi'ul Thani, 1445AH
20th October, 2023CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
#AddiniDaRayuwa #MusulunciDaRayuwa
0 Comments