Shafumulera


Idan za ku yi iskancinku, 
Ku yi iskancinku,
Ku yi rashin kunya, 
Ku yi batsarku,

Amma a addinance, a kimiyyance babu wani abu 'shafumulera', duk camfi ne. Irin wannan yana kuma faruwa tsawon tarihi har a cikin Turawa da sauran fararen fara.

Duk wanda ya yi imani hakan na faruwa, a 'psychology' mun san yana fama 'Koro Syndrome' da yake buƙatar ganin 'psychirist'. 

Camfi ne ka yi imani wani da ya saɓa da ɗabi'a zai same ka. Camfi a addini nau'i ne na shirka. Abdullahi bin Amr ya ce, Manzon Allah ﷺ na cewa, مَن ردته الطِّيَرَة عن حاجته فقد أشرك".

Allah ya tsare mana imaninmu. Ya raba mu da sharrin talauci da matsi.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments