Tauhidi


Manzon Allah ﷺ yana ƙima, girma, daraja, ɗaukaka, bawan Allah ne, ma'aikin Allah ne, duk da haka, ba a yi wa Allah tarayya da shi a wajen bauta.

Kalmar Tauhidi na nufin kaɗaitawa, kaɗaita Allah a bauta (ibada), da addu'a, da neman tsari da neman agajin gaggawa. A duk waɗannan aiyukan ba a nema a wajen wanin Allah, cikin manzanni, annabawa, mala'iku, salihan bayi, shehunnai, malamai. Da zarar ka haɗa wani da Allah a wajen waɗancan ibadodi, shi ne ake cewa shirka, ka yi shirka.

Ba wani gata, soyayya da shiriya da za a ɗora ka a addini sama da Tauhidi. Kuma kaɗaita Allah a bauta ya nufin tauyewa Manzon Allah ﷺ haƙƙi, soyayya, ko tauyewa wani malami ko shehi daraja, a'a; haka Ubangijin annabawa da salihan bayi ya tsara.

A cikin suratul An'ama, aya ta 162, Ubangiji ﷻ ya umarci Manzon Allah ﷺ cewa, ya ce: "Lalle da sallata, da baikona, da rayuwata, da mutuwa na ga Allah Ubangijin talikai. Ba shi da abokin tarayya, kuma da wancan aka umarce ni ni ne farkon masu sallamawa".

✅ Ubangiji ﷻ yana da haƙƙoƙinsa,
✅ Manzon Allah ﷺ yana da haƙƙoƙinsa,
✅ Iyayenka suna da haƙƙoƙinsu a kanka,
✅ Abokan zamanka da makwafta na da haƙƙoƙi,
✅ Kai a karan kanka kana da haƙƙoƙi da za ka kiyaye.

Ana sanin duk waɗannan a ilimi, Tauhidi (kaɗaita Allah a bauta) shi ne ilimin farko da Musulmi ya kamata ya sani. Sai ka san Allah, sannan za ka bauta masa yadda ya kamata, "الله ربي لا شريك له".

Allah ya tabbatar da mu bisa shiriya.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari 
#MusulunciDaRayuwa #AddiniDaRayuwa

Post a Comment

0 Comments