Gargaɗin kan Facebook Black Badge


⚠️ GARGAƊI

Duk lokacin da wani abu mai cutarwa yake 'trending', ana samun mutanen da suke faɗakar da mutane illar abin, amma wasu sai su yi kunne ƙashi, su yi, idan illar ta rutsa da su, su dawo suna cizon yatsa.

Ina notin kwakwalwarka? Saboda 'BLACK BADGE' ka sa 'login credential' a kan wata browser (waye mai browser? Mene ne hadafinsu?), ka ɗora VPN, ka yi wancan da wannan kawai don ka ga abu na 'trending'. Waɗanda suke kiyaye 'Community Standard' ma ya suka tsira, balle kai da kake cushe-cushe? 

Kuma idan ka sa 'BLACK BADGE', masu 'Normal Facebook' ba sa ganinsa, sai dai su ga [?] a wajen 'badge', masu 'Facebook' Lite ne ke iya ganinsa. Idan ba zaka iya biyan ₦4,500 a wata ba, ka haƙura, ba dole.

Wani lokaci, Facebook ba sa tashi tono ka, sai bayan ka manta da yin abu, sai su bunƙuɗo wani abu da ka yi da jimawa, su ma hukunci da shi, saboda ya saɓa da 'Comminuty Standard' na yanzu.

A juri zuwa rafi!

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari 
#AliyuCares #AliyuWarns #AliMotives
#FasaharZamani #Facebook #BlackBadge

Post a Comment

0 Comments