Me ya sa kake gudun abincin gidanku? Ba daɗi? Ko ba ɗanɗano?
Wai ba ka san iyayenka na jin ciwon su yi abinci ka ƙi ci ba? Suna ga sun yi iya ƙoƙarin da za su iya don su ciyar da kai, amma a aikace ka nuna, ba ka so, abincinsu bai yi ma ba, gwamma ka bar su da ƙabzarsu ka fita waje ka ci mai daɗi.
Da ₦2k da kake kashewa don siyan rabin gasasshiyyar kaza, za ka iya samun dakwaliyyar kaza 1, ko 'yan saffa 2 ka kawo gida Umma ta raɓaɓɓaka, kai ka lasa, kowa a gida ya lasa.
Da ₦1,500 da kake siyan special plate 1 a 'resturant', Mamanka ta san yadda za ta sarrafa ₦1,500 a sai kayan miya mai kyau, a yi abinci mai daɗi da kai ma za ka ci ka ƙoshi, haka waninka ma.
Da ₦1k - ₦1,500 na siyan 'shaka', 'cocktail' ko 'fruit salad', ƙanwarka a gida za ta iya haɗawa wanda kai za ka sha, Mama ta sha, sauran ƙannenka su sha.
Yanzu sai ka sayi ɗanwake a takeway 1 a ₦1k saboda an yi packaging, ko mai ɗanwake na kyau, kana ganin fararen haƙoranta duk sanda ka je? ₦1k ko ba ta isa a haɗa ɗanwake a gidanku ba, kaɗan za ka cika a sayi flour da mai, a yi ɗanwaken mutum 3 zuwa 5.
Bar ma batun mai ƙashe ₦3,500 - ₦5k don siyawa budurwa chips, kaza, shawarma, shaka, falafel, kebab, pizza... bai ci ba a cikinsa, bai kai wa iyayensa sun ci ba, ya kaiwa wacce take masa kallon dolo.
Jin daɗi matakin rayuwa ne, wani zai iya kashe ₦50k na butar shayi a 'spot', kuma normal ne, amma kai da babu tabbaci me za a ci a gidanku da safe, ka zame ka bar iyayenka da ci-mu-ƙoshi kawai, ka tafi joint cin maiƙo? Haka kake don naka 'ya'yan su ma?
Gwamma ka sadaukarwa gida, ga ƙoshi, ga albarka, ga martabawa daga iyaye da 'yan uwa. Albarkacin wannan albarkar sai ta zame ma kariya daga magauta, ga kuma ƙarin buɗi ta ko'ina albarkarcin kullum iyaye na yi ma albarka.
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments