Budurwa, da sunan soyayya, kar ka kashe mata ko sisi sai ka tabbatar mahaifiyyarka, ƙanwarka, yayarka (mace) da kai karan kanka (duk) kun wadatu da abin da za ka burge wata (mace) da shi, na abinci da sutura.
Zaɓi ya rage ma, tsakanin neman albarka da burga. Kafin ka siya ma budurwa sutura, tambayi kanka: shin mahaifiyyarka ko ƙanwarka na da irinta, ko ka yi mata? Kafin ka siyawa budurwa maƙulashe (snacks), shin kai ka ci? Wataƙila ba ma ba aurar ta za ka yi ba duk wannan burga da ɗawainiyya da kake.
Jiya na je siyan 'chips' da daddare, aboki ke cewa abokinsa ya biya masa, sai abokin ya ce, "ni ba shege ba ne, ka biya wa yarinya ₦9k na anko, ka kasa siyawa kanka abincin ƙasa da ₦1k, da mahaifiyyarka ce ta ce ka bayar da kuɗin cefane ₦1k, cewa za ka yi ba ka da kuɗi, kuma idan an dafa (ma) da kai za a ci. Ta ɗinka ankon, ta turawa sauran samarinta kwaliyya...".
Ka kashewa budurwa kuɗin da ba dole ba, ko kar ka kashe ma, idan tana sonka da gaske, ba abin da zai sauya matsayinka a wurinta; sai dai idan dama abin hannunkan take so.
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments