An haife ka a gidan masu ƙarami ƙarfi, zaɓinka ne? An haife ka a gidan mawadata, zaɓinka ne?
Da a ce nan ne gidanku (hoton ƙasa 👇), gidan laka, a tsofe, shi ne gidan da iyayenka suka gina, suka haife ka a ciki, suka rena ka har ka girma.
Kwatsam, bayan ka fara girma, sai ranka ya fara sosuwa da cewa, wannan gidan bai dace da kalar ka ba, saboa hala ka ɗan yi boko, ko fara gayu, ka fara faso gari, kana ji kamar ka fi ƙarfin wannan gidan.
Maimakon kana yawo zuwa G.R.A. da joints, da wuraren da ake parking motocin alfarma don kana ɗaukar hotuna, ka ɗorawa a social media, ga ka 'guyson', me zai hana ka fara tunanin canjawa iyayenka muhallin da kake tunani, bai dace da kai da su ba?
Kafin a ce ka ƙera naka 'duplex' ɗin daidai da zamani, ka fara tunani, fara farantawa iyayenka tun suna raye (idan suna da rai). Niyya kawai za ka ƙulla, ka sa azama. Ina maka albishir, in sha Allah, Allah zai shiga lamuranka. Ka canja labarin rayuwarka tsatsonka, za ka ga alheri, duniya da lahira.
Bai ishe ka alfahari, sana'ar da gidanku suke, hala da ita mahaifinka ya auri mahaifiyyarka, ya gidanku, ya ciyar da kai har ka girma, ya biya ma kuɗin makaranta? Ya ishe ka alfahari, iyayenka suna da ƙima da mutunci, ba su da wani mummunan tarihi, fiye da tusawa kwanyarka 'inferiority complex', just saboda ka tashi a gidan rashin wadata.
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
0 Comments