In dai har aikinka ba ya hana ka buɗe 'Facebook', ka yi 'posting' da 'comments', ko kuma buɗe 'Whatsapp', ka ɗora status, ka yi 'chatting'... TO KWA KANA DA LOKACIN KARATU.
Abin lura, idan har zaka iya zama, ka ɓata awa ɗaya (1hr) kana karanta 'comment(s)', masana suka ce; awa ɗaya ga mai ɗabi'ar karantu da sauri (fast reader), daidai take da karanta kalmomi 10,000 ko shafukan littafi 40-50 (40-50 pages) na littafi (Butler, 2014).
Shafuka 50 na iya karantuwa a wajen maras saurin karatu (slow reader) cikin awanni uku (3hrs); ga matsakaici (average) cikin awa ɗaya da rabi (1.5hrs), ga mai sauri (faster) cikin ƙasa da awa ɗaya (1hr).
1. Zaka iya tsarawa kanka karanta a ƙalla 10 pages a kowacce safiya kafin ka fita aiki ko kafin baccin dare (cikin ƙasa da 30mins). A sati, ka karanta 70 pages kenan, a wata 300 pages, a shekara 3,600 pages, a kalla za ka iya karanta littafi 1 a kowanne wata, ko littafai goma 10 a duk shekara.
2. Zaka iya amfani da lokacin sallah, kafin liman ya zo, ka karanta Alƙur'ani izu 1 (a 10 minutes), a ƙalla a kowacce rana kana tilawar izuwa 5 kenan.
Idan kuma za kana izu 1 kafin shiga sallah, da bayan iddar da sallah, hizbi 10 kenan, a kowacce rana. Cikin kwana 6, ka sauƙe Alƙur'ani Mai girma, a wata ka yi sauƙa 5 kenan.
3. Yanzu muna zamanin da kusan duk manyan littafai akwai pdf na su kyauta a shafukan internet. Na Musulunci a waqfeya.com, ko kalamullah.com, ko na boko a pdfdrive. com. Za ka iya buɗe su a lokackn cin abin ci, ko kana ɗan hutawa...
Kai! Idan ma ba zaka iya samun lokacin karatu ba, da littafan bokon, da na addinin, duk akwai su cikin sauti (audio), wasu a 'podcast', wasu zaka iya downloading.
Akwai Google Podcast:
• Android: bit.ly/3PLz5Wj
• iPhone (iSo): apple.co/3Q5PRPA
Ka sauƙe, ka sa sunan ko wannen irin littafi na boko, RICH DAD..., 48 LAWS OF POWER, POWER OF FOCUS... kowannen su, akwai su cikin sauti, sai saurara. Akwai soundcloud.com, audiable.com, sportify.com, podcasts. apple.com...
Ko kuma, ka shiga Youtube, ko Vidmate, ka sa sunan littafi, sai ka ƙara da AUDIO BOOK, ta Vidmate za ka iya sauƙe shi audio (mp3).
Ko na addini cikin harshen Hausa a darulfikr.com, kana cikin aiki, kana saurara, malamai na bayani mas'alolin addini dalla-dalla. Akwai islamicaudiobookscentral.com, learnoutloud.com...(na Turanci da Larabci).
Kar ka zauna ba ka karatu, ko ba ka saurarar karatu. Allah Ya amfana.
✍️Aliyu M. Ahmad
30th Dhul-Hijjah, 1443AH
29th July, 2022CE
#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #Karatu #GyaranTunani #AliyusLibrary #ReadingCulture
0 Comments