Salute (Gaisuwar Sojoji)


Idan sojan ƙasa (junior officer) zai gana da sojan sama (senior officer) ya masa 'salute', wanda hakan na nufin abubuwa da dama, daga ciki akwai:

1. Nufin cewa a hannun damansa babu makami (ma'ana, ba zai cutar da babban ba),*
2. Alama ce ta gaisuwa,
3. Alama ce ta girmamawa,
4. Alama ce ta miƙa wuya, sai abin da aka ce yi, za ka yi.

* A Book of Order (1745) an ambatawa sojojin Birtaniya cewa, "su sake salon gaisuwarsu, daga cire hula (hat), zuwa ɗaga hannu daidai saitin hular". Jennifer (2022) ta ce, asali an sanya wannan dokar ne, saboda a lokacin ana (yawan) samun kashe manyan sojoji. Za ka yi gaisuwa da hannu dama, hannu hagu kuma, kana riƙe da linzamin doki (ma'ana, babu abun cutarwa a hannun). Gaisauwar na nufin girmamawa da miƙa wuya.

Akwai salo kala-kala da ake 'salute' duk don nuna waɗancan dalilan na sama. Kuma duk da hannu ɗaya ake yi (na dama).

Kai kuma, idan ka zo kabbarar sallah, ba ka ga hannaye biyu kake ɗagawa a kabbara ba? Na hagun da daman?

A cikin hadisan Abdullahi ibn Umar, Abdullah bin Zubair, Salim bin Abdullah, Malik ibn Al-Huwayrith da wasunsu رضي الله عنهم cewa, Manzon Allah ﷺ ya ɗaya hannayensa 2 a lokacin:

1. Kabbarar harama, 
2. Kafin tafiya ruku'u, 
3. Ɗagowa daga ruku'u, da kuma
4. Ɗagowa daga zaman tahiyar farko.

Mun san ɗaga hannu a sallah sunnah, amma shin mun san dalili ɗaga hannun a ruhaniyya? 

Ɗaga hannu a sallah alama ce ta girmamawa da miƙa wuya. Ibn Qayyim Al-Jawziyya (691AH - 751AH) cikin I’lam Al-Muwaqqi’in (2/376) ya ce, a lokacin sahhabi, idan Abdullah Ibn Umar ya ga wani yana sallah ba ya ɗaga hannu, sai ya jefe shi da tsakuwa.

Ita kuma sallah, gaba ɗaya ta gani ce da Ubangiji ta ruhi. Har ya tabbata daga Abdurrahman ibn Sakhr (Abu Huraira) cikin hadisul ƙudsi, Ubangiji ﷻ na cewa "قسمت الصلاة بيني وبين عبدي نصفين...", yana raba sallah tsakaninsa da bawa, duk abin da ya ambata na karatun Fatiha, Ubangiji yana amsa masa.

Ya kake jin ɗanɗano a ruhinka idan kana sallah? Ka taɓa tunani, ko sanin dalilin da ya sa kake ruku'u, sujjada, zaman tahiya, da sauran rukunan sallah?

✍️Aliyu M. Ahmad
14th Rabi'ul Awwal, 1445AH
29th September, 2023CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives
#MusulunciDaRayuwa #AddiniDaRayuwa

Post a Comment

0 Comments