Dalilin Shiriyata


#AliyusDiary

Ya ce: "Abin da na yi imani shi ne silar shiriyata...

Lokacin da muka taso da abokina, mun yi shirin fara shaye-shaye, tabbas a lokacin mun biya wasu abokanmu, har mun fara shiga 'jungle'.

Da aka kawo ƙara ta wajen Mamana, abin da ta fara cewa mutumin nan, ina ji ta ce "Na gode Malam! Allah ya shirye Khalifa, ya raba shi da abokan banza". 

Da dare ya yi, Mama ta kasa zama, ta kasa tashi, ta je ƙofar ɗakina, ta juya. Ina ganinta sintiri hankali ya tashi. Na fito na ce, "Mama, ni kam lafiya, tun ɗazu na lura sai kai kawo kike..."

Mama ta ce, "Ba dole hankali ya tashi ba, an ce min kana neman biyewa abokan banza ka lalace. Mahaifinku ya rasu, kai ne namiji da ya kamata ka kama kanka, ka yi hankali, saboda a gaba kai ne mai riƙe gida. Idan ka lalace, wato kai ma sai dai ka zame mana nauyi. Ba dole hankalina ya tashi ba. Don Allah ka ji tsoron Allah, kar ka samin ciwon zuciya..."

Tun daga lokacin na ji abin ya fita min a rai. Alhamdulillah, a lokacin ban yi nisa ba. Kuma tun washegari, ina ga Mama ta dafa abinci ta yi sadaka. Tun wannan lokaci duk safiyar Juma'a sai ta yi abincin sadaka. Ban kuma taɓa tashi da daddare ban ga Mama tana sallah ba. Na yi imani, Mama duk don ni take yi.

Shi kuwa abokin nawa, lokacin da aka kai ƙararsa gida, Mamansa faɗa ta fito tana yi, wai za a yi wa ɗanta sharri. Ga 'ya'yan unguwa nan suna abin da suka dama sai nata za a sa wa ido. Haka ya ci gaba zuwa 'jungle', ni kam na ma fita a harkarsa. Idan ya yi ta'asa, aka kawo ƙara gida ma a banza, don babarsa za ta kare shi (kai mai kawo ƙarar ma, sai a ce ma magulmaci), kuma ba ta masa faɗa (ba jan kunne ko nasiha). Shi mahaifinsa yana raye, amma ba sa tare da mahaifiyyarsa, a wajenta yake...

Darasi

Tabbas, iyayenmu suna da tasiri a shiriyarmu, haka za su iya tasiri wajen lalacewarmu.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari 
#AliMotives #AliyusMemoir

Post a Comment

0 Comments