KA SAURARI WANNAN MURYAR!

Duk lokacin da ka ji ana cewa, wane ba ka kyautawa, ko kana wani abu ba daidai, just listen, wataƙila hakan ne, kai ne ba ka lura ba. 

Ka nutsu, 
Ka yi nazari, 
Ka gyara.

Duk lokacin da ake cewa, wane abu kaza ba addini ba ne, shirka ne, ko bidi'a, just listen, yi ƙoƙarin jin mene ne dalilin haramta wannan aikin? Mene ne hujjar da ya sa kake aikatawa? Idan ka yi binciken ilimi da buɗaɗɗiyar zuciya, duk abin da ka fi gamsuwa da shi sai ka riƙe.

Duk lokacin da aka ce kana da wata halayya maras kyau, ba faɗa zaka yi ba, ai kai ba MALA'IKA ba ne, MUTUM ne; kuskure yana daga cikin ɗabi'ar mutum, ka saurara, ka duba kanka, ka gyara.

Duk lokacin da ka yi wani zaɓi, ka ji muryoyi na cewa, ba ka dace da wannan zaɓin ba, misali, neman aure. So kan rufe idon mai so, ya manta da abin da yake buƙata, ya zaɓi abin da ya fi so. Ka nutsu, ka saurara, kada daga baya kana cewa, dama an faɗa min, bayan lokaci ya ƙure maka.

A duniyar yau! 

Ba wani mutum da yake duk tarin iliminsa ko wayewarsa da ba ya wani abu na kuskure, a aiki, ko a ɗabi'a. NORMAL ne ka rayu tsawon lokacin cikin kuskure. WINNING ne, ka gane a baya kana kusakurai, a yanzu kuma za ka gyara.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari #AliMotives

Post a Comment

0 Comments