Salati


Don Allah ku daina yaɗa bidiyon gayen nan, wai salatin da aka ruwaito a ɗarikarsa ya fi wanda aka laƙalto daga Manzon Allah ﷺ kai-tsaye (ba tare ya yi inkarin isnadinsa na Manzon Allah ﷺ ba).

Wallahi wannan raini ne tsantsa ga janibin Ma'aiki ﷺ, a aikace kuma, ƙaryar son Manzon Allah ﷺ ce a baki, fifita wani sama da Ma'aiki ﷺ. Ba wanda ya ce kar ka yi wa annabi salati da yabo da kalmomi masu kyau.

A lokacin da aka saukar da aya ta 56 cikin Ahzab "إن الله وملائكته يصلون على النبي يا أيها الذين آمنوا صلوا عليه وسلموا تسليما"

Sahabban Manzon Allah ﷺ, ba su fara salati ba sai da suka tambaye shi ﷺ, cewa:  "يا رسول الله، قد علمنا الله كيف نسلم عليك؛ فكيف نصلي عليك؟" a nan ya koyar da su cewa, idan za ku min salati, ku ce:

"اللهم صل على محمد، وعلى آل محمد، كما صليت على إبراهيم، وعلى آل إبراهيم، إنك حميد مجيد، وبارك على محمد، وعلى آل محمد، كما باركت على إبراهيم"

Wannan shi ne salatin Ibrahamiyya. Akwai sauran salatai da aka ruwaita da wasu sigogin ingantattu.

A cikin Rawdatut Taalibin, Imam Yahya Bin Sharaf Al-Nawawi (631 - 676AH) cikin falalar salati, ya kawo hadisin Abu Humayd As-Saa‘idi رضي الله عنه yake cewa,

وهو عليه الصلاة والسلام لا يختار إلا الأشرف والأفضل

"Manzon Allah ﷺ ba ya zaɓe sai wanda yake mafifici da falala".

Idan cikar kalmomi ne masu daraja, 'Dala'il Al Khayrati' ya fi 'Salatil Fatih' kalmomin yabo. Ko ba komai, wanda yake daga Ma'aiki ﷺ kai-tsaye mu ya fi mana. Kar a ruɗe ka da wata falala, kana ganin ƙasƙancin abin da Ma'aiki ﷺ ya zo da shi, kana ƙimantawa wani wahayin da ba a kallafa ma imani da shi ba.

Don Allah kana ikirarin son Manzon Allah ﷺ, wani ya yi wannan kwaɓar, har ka fito da kwarin gwuiwar kana kare shi? Ina soyayyar? Ina hankalinka?

هذه سبيلي أدعو إلى الله على بصيرة أنا ومن اتبعني وسبحان الله وما أنا من المشركين

Ba mu yi wa Allah ﷻ kishiya a bauta. Ba za mu yi wa Manzon Allah ﷺ kishiya a bi da soyayya ba.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari 
#MusulunciDaRayuwa #AddiniDaRayuwa

Post a Comment

0 Comments