𝗞𝗮𝗻𝗮 𝘀𝗼𝗻 𝗸𝗮 𝘀𝗮𝘆𝗶 𝘄𝗮𝘆𝗮?

Idan ka so siyan waya, tambayoyi 2 ne masu muhimmanci ya kamata ka amsawa kanka:

1. Mene ne dalilin siyan wayar?
2. Nawa ne 'budget' ɗinka? 

⚠️ Kar ka taɓa sanya dalilin son burge mutane (social validation) ko gasa da abokai shi ne dalilin siyan wayarka.

𝟭𝗮. Kana son siyan waya ne don kasuwancinka ne? Ko kai ɗalibi ne don karatu da browsing? Ko content creators ne kai? Social media manager? Trading, coding, data entry, gaming...? Burga (fashion da packaging) za ka yi da waya?

𝟭𝗯. Me ka fi buƙata da waya? Ƙiran waya? Network? Camera? Storage? Battery? Chipset ko RAM? OS? Burga?

• Ƙ𝗶𝗿𝗮𝗻 𝘄𝗮𝘆𝗮

Idan don iya ƙiran waya kake so waya, akwai wayoyi masu bada sauti ƙira raurau, su kuma rage hayaniya (noise cancellation) da tace murya a lokacin waya, misali iPhone, Google Pixel, Samsung Note da S series. Ko kuma ka yi amfani da Samsung Buds Pro ko Airpod (original).

• 𝗡𝗲𝘁𝘄𝗼𝗿𝗸

Akwai wanda yake buƙatar waya don amfani da network, Samsung S da Note series, iPhone, Pixel, OnePlus, Xiaomi 12/13 Ultra, duk suna da GSM, CDMA, HSPA (3G), EVDO da LTE (4G), wasu models kuma suna da 5G network. Yawancin 'budget phones' ba su da CDMA da EVDO wanda yana taimakawa network na waya sosai.

• 𝗖𝗮𝗺𝗲𝗿𝗮

iPhone, Google Pixel, Samsung S da Note Series, Tecno Phantom, Infinix Zero, Oppo Find X... duk cikin rukunan nan, ba dole sai 'latest' ba, duk series ɗinsu suna da camera mai kyau. Misali, Pixel 3 (₦75k+), ko iPhone 6 (₦50k+), ko S8 (₦70k+).

• 𝗦𝘁𝗼𝗿𝗮𝗴𝗲

Idan buƙatarka storage ce, a Tecno, Infinix da Redmi na ₦150k+, za ka sami mai 256GB storage.

A storages, akwai NVMe na kan iPhone da UFS storage kan 'android flagship phones' ya fi sauri a 'cable transfer'. eMMC shi ne yawanci a kan wayoyin Infinix da Tecno da sauran 'budget phones'. Latest eMMC 5.1 yana gudun 250MB/s, wanda shi kuma UFS 4.0 yana gudun 4200MB/s; hatta UFS 3.1 yana 1200MB/s (ai ba haɗi). 

Hatta a USB-type akwai 2.0, da 3.1/3.2. USB 2.0 irin na kan 'budget phone,' yana harba 480Mbps, kuma ba kowanne irin OTG yake karɓa ba. USB 3.0 yana harba 4.8Gbps, 3.1 yana 10Gbps, 3.2 kuma 20Gbps a 'cable transfer'.

• 𝗕𝗲𝘁𝘁𝗲𝗿𝘆

Samsung M series, ko Tecno Pova series, Infinix GT ko Hot series (amma Play), Redmi Prime, sune masu batir 6000/7000mAh. Akwai masu 5000mAh Camon series, Infinix da Redmi Note series, Samsung A series da sauransu.

A sake kula, bayan batir, akwai WAT na caji daga 18W zuwa 120W. Misali, Infinix Note 30 tana cajin 45W da 5000mAh batir, za ta iya cika a ƙasa da 1hr. Akwai kuma wayoyin da suke da 'wireless charging' da 'magsafe', kamar iPhone, Google Pixel, Samsung A da Note series, Infinix Note 30 Pro, wacce ba buƙatar jona USB-cable, sai dai ka kara waya ta baya a kan farantin 'wireless charger'.

• 𝗖𝗵𝗶𝗽𝘀𝗲𝘁

Chipset ke sa waya buɗe abubuwan waya da sauri, RAM kuma ke taimaka wajen amfani da 'apps' da yawa a lokaci guda ba tare da waya na ƙamewa ba.

A chipset daga Apple Bionic, sai Samsung Exynos, MediaTek Dimensity, Qualcomm Snapdragon, Google Pixel Tensor, Huewei Kirin... zuwa Mediatek Helio irin na kan Itel, Infinix da Tecno.

RAM kuma ka duba daga 6GB, 8GB+, kar ka ruɗu da Infinix da Tecno da ake sa musu 16GB, 8GB ne na haƙiƙa, sauran 8GB expandable ne (ko a Samsung S series Ultra ke da 12GB ko 16GB RAM). Kuma Samsung mai 6GB tafi Infinix/Tecno mai 8GB.

• 𝗢𝗽𝗲𝗿𝗮𝘁𝗶𝗻𝗴 𝗦𝘆𝘀𝘁𝗲𝗺 (𝗢𝗦, 𝗶𝗢𝗦/𝗔𝗻𝗱𝗿𝗼𝗶𝗱)

Idan don 'operating system' kake son waya, ka duba mai karɓar 'update', wacce za ka iya tafiya da ita shekaru da yawa. Misali, iPhone XR ta fito da iOS 12 tun 2018, yanzu kuma za ta iya karɓar iOS 17 irin na kan iPhone 15. Ko Samsung S20, ta fito da Android 10 a 2020, za ta iya karɓar Android 13 da One UI 5 irin na san Galaxy S23. Irin waɗannan ba ka buƙatar canjin waya a kurkusa.

• 𝗕𝘂𝗿𝗴𝗮 (𝗳𝗮𝘀𝗵𝗶𝗼𝗻 𝗸𝗼 𝗽𝗮𝗰𝗸𝗮𝗴𝗶𝗻𝗴)

iPhone ita ce ɗaya a burga, sai Samsung Fold ko ZFlip, ko Tecno Fold, Google Pixel Fold, Motorola Razr, Oppo Find N, Honor Magic.. amma duk sai ka tanadi sama da ₦450k.

𝟮. 𝗡𝗮𝘄𝗮 𝗻𝗲 𝗸𝗮𝗸𝗲 𝗱𝗮 𝘀𝗵𝗶 𝗮 𝘆𝗮𝗻𝘇𝘂 𝗱𝗮 𝘇𝗮𝗶 𝗯𝗶𝘆𝗮 𝗺𝗮 𝗯𝘂ƙ𝗮𝘁𝗮𝗿 𝘀𝗮𝗺𝘂𝗻 𝗮𝗯𝗶𝗻 𝗱𝗮 𝗸𝗮𝗸𝗲 𝘀𝗼? 

Akwai '𝗯𝘂𝗱𝗴𝗲𝘁 𝗽𝗵𝗼𝗻𝗲𝘀' 
Akwai '𝗳𝗹𝗮𝗴𝘀𝗵𝗶𝗽'

Budget phones wayoyi ne masu sauƙin kuɗi, kamar Airtel, Tecno, Infinix, Xiaomi Redmi da Note series, Samsung A da M series da sauransu. Yawanci suna fara daga ₦50k+ zuwa ₦250k+.

Flagship rukunin wayoyi ne masu tsada saboda 'specs' nasu na musamman ne. Misali, iPhone, Samsung Note da S series, Google Pixel, Vivo iQOO da X series, ko Tecno Phantom da Infinix Zero. Kuɗinsu yana farawa ne daga ₦350+ har zuwa sama da ₦1m.

Bayan wancan nazari, a aljihunka kana da ₦150k, kana da zaɓi 2 a siyan waya, ko ka sayi sabuwa (budget phone), ko ka sayi London Used (2019/2020 flagship phone). 

Da ₦150k za ka iya samun Dubai/London na iPhone XR, X, Xs ko Samsung S10/S10+ ko Note 10 (normal), Google Pixel 4/4XL, Tecno Phantom X da sauransu. Ko kuma ka sami Infinix Note 30 5G/30 (256GB), Tecno Camon 20, Xiaomi Redmi 12 ko Note 12, ko Samsung A23. 

Idan kuma kana buƙatar ganin 'specs' na kowacce waya kuma, ko muƙaranarta (comparing) da wata, ka shiga GSMArena, ko ka shiga shafin Eric Okafor, Valor Reviews, Izzi Boye, Fisayo Fusodu, Tech Rann... a Youtube ko TikTok. Suna unboxing waya da bada reviews a zahiri.

✍️𝗔𝗹𝗶𝘆𝘂 𝗠. 𝗔𝗵𝗺𝗮𝗱
29th Safar, 1445AH
15th September, 2023CE

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari 
#aliyusphone #FasaharZamani

Post a Comment

0 Comments