Sabuwar Ibada


Za ka iya gane fiƙhun wani 'PONZI SCHEME' da ya gabata? Masana da sauran mutane na faɗawa mutanen da suke 'investing' cewa za a zalunce, mutanen nan za su gudu; amma har zagi da cin mutuncin waɗanda suke faɗa musu gaskiya suke don kare wannan 'scheme' ɗin, saboda suna samun kuɗi/riba a lokacin.

Kamar haka ne a wasu mas'alolin addini, masana, waɗanda suke gane gaskiya na cewa wata ibada babu kyau, ba ta da asali, halaka ce, ba addini ba ce; amma wasu da suka tsunduma cikinta suna da kwarin gwuiwar kare fahimtarsu da magabatansu.

Na farko, suna iya gani aya a zahiri, da uƙuba ta asara da guduwar 'con artists', tukun; sai su fahimci gaskiyar da ake faɗa musu. Na biyu, masu addini (wasu) ba su ganin laifi ko halaka har sai an tsaya ranar sakamako, saboda suna samun nutsuwa da ibadodin da suke a yanzu. Kamar na farko, mutane sun dage ne saboda suna samun riba, haka na biyu (na addini) mutane suna dagewa ne saboda alƙawarin samun wani sakamakon lada ne.

Gaskiya ƙarya ne, wani mutum a bayan Annabi ﷺ ya kawo wata ibada, ka ce wai tafi wacce Manzon Allah ﷺ ya kawo (lafiyayyen hankali ba zai ɗauka ba), kuma (wai) kana ikrarin kana son Manzon Allah ﷺ. Kamar shugaban ƙasa ya bada umarni ne, ka ce kai maganar kansilar unguwar za ka ɗauka (wannan kwatancen ma ya yi kusa da yawa). Gaskiya na zuwa ga wanda ya shiryawa ɗaukarta.

Allah ya datar da mu bisa shiriya.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari
#MusulunciDaRayuwa #AddiniDaRayuwa

Post a Comment

0 Comments