Idan Sunnar Annabi ﷺ Kake Son Bi...


Idan SUNNAR MANZON ALLAH ﷺ kake son ɗabbaƙawa a rayuwarka, ka karanta tarihin da shama'ila na Manzon Allah ﷺ, kana kwatantawa a aikace.

Ka karanci mu'amalarsa da mutane Makkah kafin annabbata. Ka karanci yadda ya rayu da Yahudawan Madinah.

Ka karanci mu'amalarsa da mata da ƙananan yara. Ka karanci karamcinsa, tausayinsa da kawaicinsa.

Ka karancin yadda yake rayuwa, ibada, wuridi, cin abinci, bacci, tafiya, zama...

1. Anas Ibn Malik (7BH - 98AH) ya ce, watarana wani mutumin ƙauye ya zo ya yi fitsari a masallacin Madinah, Sahabbai suka taso masa, Manzon Allah ﷺ ya ce Ku bar shi, idan ya kammala ku zuba ruwa a wajen (Muslim, 285).

2. Kafin a yi hijira, a Makkah wata mata Bayahudiyya kullum sai ta zuba shara ƙofar gidan Manzon Allah ﷺ. Ranar da ta yi jinya ba ta zuba sharar ba, Manzon Allah ﷺ ya je ya gaishe ta, wannan halin kirki ya sa ta karɓi Musulunci.

3. Nana Aysha رضي الله عنها ta ce, ba ya daga cikin halayyar Manzon Allah ɗaga murya ko kausasa kalmominsa (Shama'il, 330). 

4. Anas ya ce, Manzon Allah ﷺ bai taɓa ajiye wani abu don gobe ba. Ma'ana, idan ya sami abinci rabawa yake ga mabuƙata.

5. Ka san dalilin musuluntar Ghaurath ibnul Harith?  Attacking Manzon Allah ﷺ ya yi da takobi a lokaci yana kwance a ƙasan bishiya, ya gaza, Manzon Allah ﷺ ya zaunar da shi ya yafe masa. Ba don Manzon Allah ﷺ ya yafe masa, a wurin da su Jabir bin Abdallah (16BH - 78AH) sun sille shi. Kai ya kake idan wani ya zage ka ko ya ci mutuncinka? Ka kafa majalisi ka rama ko?

6. Manzon Allah ﷺ ya ce, an aiko shi don ya cika kyawawan halaye (Adabul Mufrad, 273).

Shin haka kake? 
Kana kwatantawa?

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari

Post a Comment

0 Comments