Reality


• Kuɗin aikin Hajji bana (1445AH), zai kai 4.5m, wanda a baya 1444AH (2022/2023), 2.6m ne 'initial payment', za a sami ƙarin kusan 1.9m.
• Makarantu suna ƙara kuɗaɗe, a hakan ma wasu wuraren somin taɓi ne (suka ce),
• Kana nufin manoma shinkafar bana za su sauƙo ma da ita kwana #1k? A yadda aka yi noma da wahala, taki tsada, man fetir tsada.
• Wane abu ne da farashin bai tashi ba, bai sauya ba a kasuwar yau?
• Kullum darajar ₦aira ƙara lalacewa yake, a cikin kwana 100, daga May, 2023 zuwa yau, nawa ne ya ƙaru a farashin $1 zuwa ₦aira? 

Masani ya yi magana ta ilimi da tajriba, ya ce wahala tana ƙara zuwa matuƙar ba ɗauki mataki ba, MU YI TANADI, MU NEMI MAFITA, amma kuna zaginsa kuna ƙorafi maimakon tunanin neman mafita. Kana ƙin gaskiyar Masani ne saboda adawar siyasa, ko ƙungiyancin addini, ko saboda ƴar tsama tsakanin talaka da masu kuɗi (social conflict)...

...duk kana ta ƙorafi, a yau:

Wani ya yi sabon aure, 
Wani ya gina sabon gida, 
Wani ya sayi sabuwar mota, 
Wani ya gina sabon masallaci sadaka, 
Wani ya sayi irin wayar da kake mafarki,
Wani ya ɗinka irin sabuwar sutura...

... Saboda bai zama cikin masu ƙorafi ba, ya kasance cikin masu karɓar 'reality', sun adjusting don nema daga falalar Allah, kuma suna samu.

Yi amfani da hankali!
Allah ya kawo sauƙi.

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari
#AliMotives

Photo credit: Take Profit

Post a Comment

0 Comments