Jan Carbi


Ko mene ne amfanin dawo da jayayya kan amfani da tasbaha (carbi), oho! 

Wani ko gama sanin hukunce-hukunce tsarki da sallah bai gama. Ga farali ba ka gama sani ba da kyau, sai kya hau rigima da mutane kan carbi? Idan ka GAMSU za ka iya AMFANI da shi, ka yi AMFANI da shi. Idan BA KA GAMSU da amfani da 'tasbaha' ko 'counter' ba, ka TSINKA ka JEFAR. Simple!

Wani lokacin, muna da tarin ilimi da kishin addini da sunnah, amma akwai ƙaranci tarbiyya ilmiyyah. Mene ne idan kana da fahimta da hujja a ilimi, idan za ka iya bayaninsa sai ka fasiƙantar, ko jahiltar, ko ka tunzura wanda kake son ilmantarwa? 

Shi ya sa idan ka yi karatu wajen dattawan malamai, za su koya ma tarbiyya. Wasu abubuwan ba su kai a tada jijiyar wuya a kansu ba, sai ka ga an maida shi cin mutuncin juna sai ka ce 'cavilers'. Watarana an gama majalisi, sai wani yake cewa Malam Isa Waziri (Allah ya jiƙan rai), "Malam wani ya zagi carbi?" Malam ya ce, "ina carbi?" Aka miƙo masa, ya ce "carbi uwaka, uwaka carbi".  Mene ne abin tada hankali, tada jijiyar wuya da cin mutuncin juna? 

#AliyuMAhmad #RayuwaDaNazari 
#MusulunciDaRayuwa #AddiniDaRayuwa

Post a Comment

0 Comments